Idan an zāɓi yin wannan salla, a bāyan an yi arwalla, a tāshi, a jūya gabā gabas maso arēwa, a dūbi dāma da hauni, tamkar mai nēman rahamar Ubangiji, ar-rahamane, mai jinƙai, kuma a cē :
Yā kai wanda kai nē Ubangijin duka sunāyē, kuma mahaliccin sammai ! dōmin darajar waɗanda sū nē asubāhin zātinka mai girma, ma fi ɗaukaka, da ya wuce a gāne Shi, ina rōƙon ka sā sallāta, ta zamana tamkar wutar da zā ta ƙōnē yānar dake hanā ni ganin kyāwonka, kuma ta haske hanyāta zuwa tēkun kusantarka.
A ɗaga hannuwa wajen Ubangiji, yabo da ɗaukaka su tabbata a garēshe, a cē:
Yā kai buƙātar dūniya, gātan duka al’umma, kana gani nā jūwa huskāta wajenka, cikin wātsi da duka wata dōgara ga kōwa in bā kai ba, kuma riƙe da igiyarka wadda mōtsinta nē yake mōtsa halitta gabāɗayanta. Yā kai Ubangijina, nī bāwanka nē, kuma ɗan bāwanka. Kana gani nā shirya cika ƙudurarka, kuma da abun da kake sō. Bā nā son kōmai, sai abunda kake sō.
Ta hanyar tēkun rahamarka da rānar alfurmarka, ina rōƙon ka ɗōrāwa bāwanka abun da kake sō, da ya dāce a garēka. Nā rantse da īkonka da ya wuce kwatamci da kirāri, duka abun da ka bayyana, shīnē gūrin zūciyāta da abun ƙaunar rūhūna.
Yā Allah Ubangijina, kada ka dūbi nufīna kō aikīna, amma ka dūbi īkonka wanda ya lulluɓe sama da ƙasa. Yā kai Ugangijin duka al’umma, da sūnanka mafi girma, bā na buƙātar kōmi, in bā abun da kake buƙāta ba, kuma bā nā son kōmi in ba abun da kake sō ba.
A durƙusa, kuma gōshi bisa ƙasa a cē :
Ɗaukakarka tā wuce duk wani kwatamci wanda bā nāka ba, kuma tā wuce fahimtar kōwa in bā tāka ba.
A tāshi, a cē :
Yā Ubangijina, ka maida sallāta marmaron ruwa garai da zā ya rāyar da ni har abada, kuma sallar nan, ta sā in ambacē ka cikin kōwace dūniyarka.
A tāshi, kuma a ɗaga hannuwa cikin rōƙo, a cē:
Yā kai da kake zāzafa zūkāce da rūhunnai idan sun nīsanta da kai, kuma da kake haske dūniya gabāɗayanta da hasken sōyayyarka! Da sūnanka mai sanyaya duka ran halitta, ina rōƙon kada ka hanā mani duka abun da yake nāka, yā kai mai īkon duka ƴan adam! Yā Ubangijina, kanā ganin wannan bāƙon yana gaugautāwa wajen mabartarsa mafi ɗaukaka, ƙalƙashin runfar martabarka, gaban bangon rahamarka, wannan mazunubanci da yake nēman tēkun gāfararka, wannan ƙasƙantacce da yake zuwa nufa fādar ɗaukakarka, wannan miskīni da yake nēman arzikinka.
Kai kake umurta abun da kake sō! Nā shaida cēwa, yabo yā cancanca ga duka ƙudurarka da abun da ka aikata, kuma cikkaken ƴinci yā tabbata ga dokokinka.
A ɗaga hannuwa, a jā “Allah’u’Abha” sau uku. A dūƙa gaban Ubangiji (albarka da yabo su tabbata a garēshi), a ɗōra hannuwa bisa gwiwōwi, a cē :
Yā Allāna, kana ganin yanda dukāna nake cike da buƙātar yabonka, da kuzārin kiran sūnanka, kuma da yaba ka; kana ganin yadda rūhuna yake fadaƙar da abun da harshen dōkarka ya ƙayyada cikin daular kalmarka, kuma bisa samāniyar iliminka. Yā Ubangijina, cikin wannan hālin da raina yake, ina ƙaunar tambayarka duka abun dake nāka nē, tunda nī maskīni nē, ina ɗaukaka alhērinka da arzikinka, tunda nī talakka nē, ina tabbatar da īkonka da ƙarfinka.
A mīƙe, kuma a ɗaga hannuwa sau biyu, a rōƙi cēwa:
Bābu wani Allah sai kai, mai ƙudura, mai yalwā maras iyāka. Bābu wani Allah sai kai, ma’umurcin farko da na ƙarshe. Yā Ubangiji Allāna, afuwarka tā bāni kuzāri, kuma rahamarka tā ƙarfafa ni; kiranka yā falkar da ni, alfurmarka tā ɗaga nī zuwa garēka. Idan bā haka ba, ta yāya zā ni tarki tsayāwa ƙōfar fādarka, kō kuma in ɗaga fuskāta wajen hasken dake ƙyalƙyali daga samāniyar ƙudurarka ?
Yā Ubangijina, kana ganin wannan miskīni yana ƙyarƙyara ƙōfar alfurmarka, wannan rūhu nā nēman ƙōramar rāyuwar har abada, daga cikin hannun yalwarka.
Yā kai Ubangijin duka sunaye, īko yana garēka kōwane lōkaci, nī kuma haƙuri da ladabi ga ƙudurarka, sū nē nāwa, yā mahaliccin sammai !
A ɗaga hannuwa sau uku, a cē:
Allah shīnē mafi girma!
A ɗurƙusa goshi a ƙasa, a cē :
Ɗaukakarka tā wuce matsayin da yabon māsu kusantaka da kai, ya isa samāniyar fadarka, kō tsuntsāyen zūkācen masōyanka su kai ƙōfarka.
Nā shaida cēwa, tsarkakarka tā wuce kōwane laƙani da kōwane sūna. Babu wani Allah sai kai, mai mulki, maɗaukakin sarki.
A zauna a cē :
Kamar duk halittu, malā’ikun samāniya, mazaunan aljannar ƙōli, kuma sama da su, mazaunan sararin samāniyar ɗaukaka, da harshen martaba shi da kansa, nā shaida cēwa, kai nē Allah, bā ka da abōkin tārayya, kuma wanda ka manzonta shīnē, bōyeyyen gaibu, shīnē alāma mai daraja. Ta garēshi aka haɗa baƙaƙe k-a-s-a-n-c-e (kasance), kuma aka haɗā su, aka ɗaure su.
Nā shaida cēwa, sūnansa nē alƙalamin ƙudura da irāda ya rubuta, kuma aka ambata cikin litattafan Allah Ubangijin karagun sama da ƙasa.
A tāshi a cē :
Yā kai Ubangijin duk halitta, kuma mamallakin duka abūbūwan da ake gani kō dake ɓōye, kana ganin hawāyēna, kana jin nīshīna, kana jin kūkāna, gungunīna da takaicin dake zūciyāta. Don girmanka, laifuffukāna suna hana ni kusanta da kai, kuma zunubaina, nā nīsantā ni da tsarkakarka.
Yā Ubangijina, ƙaunarka nā arzitar da ni, rabuwa da kai nā hallakā ni, kuma nīsanta da kai, nā tōya ni rumus. Da sūnan sāwunka cikin hamāda, ta wannan kalmōmi «gā ni, gā ni !» da gātāyanka suke faɗa cikin sarari, da sūnan numfāshin bayyanarka, da iskar sāhiyar wahayinka, ina rōƙon ka yarda, in kalli kyāwonka, kuma in bi duka abun dake cikin kitābinka.
A jā Allah’u’Abha sau uku, a ɗūka, hannuwa bisa gwīwōwi a cē :
Yabo ya tabbata a garēka yā Allāna! kana taimako nā da tunāni da kai, kuma da yabāwa da kai. Kana sanarshe ni da wanda shīnē assubāhin āyōyinka. Kana sā ni dūƙāwa gaban īkonka, durƙusāwa gabanka, kuma da yarda da abunda harshen girmā ya ayyana.
A tāshi, a cē :
Yā Allah Ubangijina, nauyin zunubaina yā sā na yi dōro, kuma sakacīna yā hallakā ni. Idan na yi nazari bisa laifufukāna da alhērinka, zūciyāta sai ta kātse, jikīna ya yi sanyi. Yā kai abun shāwar duka dūniya, dōmin kyāwonka, sai na ji kunyar ɗaga fuskāta wajenka, kuma na ji kunyar ɗaga hannuwāna, dōmin rōƙo wajen samāniyar alhērinka.
Yā Allāna, kana ganin yanda hawāyēna suke hana mani ambatar ka da yaba iyāwarka, yā kai Ubangijin karagun sama da ƙasa! Don sabōda alāmun īkonka, kuma da gaibun daularka, ina rōƙon, ka dūbi masōyanka da idon alfurmarka, yā kai sarkin abūbūwan da ake gani da na ɓōye.
A jā Allah’u’Abha sau uku, a durƙusa, gōshi a ƙasa a cē :
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allah! Kana bayyana muna abun da yake kusantar mu da kai, kuma kana bā mu duka alhērin dake cikin litattafai da kitābōbinka.
Yā Ubangijinmu, muna rōƙon ka kāre mu da rundunar tunāninmu na wōfi, da ra’āyōyinmu na shirme. A gaskiya, kai nē mai ƙudura, masanin kōmi.
A tāshi tsaye a ce:
Yā Allāna, nā shaida abūbūwan da gātāyanka suka shaida, kuma nā faɗakar da abun da mazaunan aljanna, da waɗanda suke kēwaye da karagar fādarka, suka faɗakar. Daulōlin ƙasa da na sama duka nāka ne, yā Ubangijin dūniyōyi.
Idan an zāɓi yin wannan salla, a bāyan an yi arwalla, sai a jā wannan āyā da sāfe, da rāna, kuma da dare kōwace rāna.
Ana tsaye, a jūya fuska wajen ƙibla, a cē :
Allah yā tabbata cēwa, bābu wani Allah sai Shi. Daulōlin wahayi da halittu duka nāsa nē. A gaskiya, yā bayyana wanda shīnē asubāhin wahayi, wanda ya zanta bisa sinaï, wanda ta garēshi maɗaukakin haske ya haska, wanda ta garēshi itāciya mai martaba wanda bāyanta bābu wata hanya, kuma wanda ta garēsta aka yi wannan kira zuwa ga duk waɗanda suke sama da ƙasa cēwa: «Gā wanda shīnē mai kōwa mai kōmi yā iso. Ƙasa da sama, ɗaukaka da ƙudra mallakar Allah nē, Ubangijin duka ƴan adam, kuma mai mallakar mulkin sama da na ƙasa. »
A dūƙa, hannuwa bisa gwiwōwi, a cē:
Kā fi ƙarfin yabōna da yabon kōwa, kā fi ƙarfin kwatamcina kō na duk mazaunan sama da ƙasa!
Kuma a tāshi tsaye, hannuwa a būɗe wajan fuskā, a cē:
Yā Allāna, kada ka yi wātsi da wanda yake mīƙa hannuwan rōƙō a garēka, sarƙafe ga rīgar rahamarka da karāmarka, yā kai mafi rahama cikin māsu aikata rahama.
A zauna a cē :
Nā tabbata cēwa, da kai kaɗai kake, kuma bā ka da abōkin tārayya, kai nē Allah, kuma bābu wani Allah sai kai.
A gaskiya, kā bayyana addīninka, kā cika alkawalinka, kuma kā būɗa ƙōfar alfurmarka warai, ga duk waɗanda sukē sama da ƙasa. Albarka da sallama, tsīra da ɗaukaka, su tabbata ga masōyanka, waɗanda sauye-sauye da harakōkin dūniya, ba su hana su ba jūyāwa wajenka, kuma waɗanda suka yi wātsi da duk abūbūwansu, dōmin su sāmu abunda kē tāre da kai.
A gaskiya, kai nē mai jinƙai har abada, mai yalwa.
Idan an fi sō, ana iya karanta waɗannan gajērun āyōyi, kambacin waɗanda kē bāya; ana tsaye a cē:
Allah yā tabbata cēwa, bābu wani Allah sai Shi, mai cēto cikin matsala, mabuwāyi.
Ana zaune, a cē :
Nā tabbata da kai kaɗai kake, bā ka da abōkin tārayya, kai nē Allah, kuma bābu wani Ubangiji sai kai.
Idan kā zāɓi yin wannan salla, a bāyan kā yi arwalla, sai ka jā wannan āyā tsakānin tsakiyar rānā da fāɗuwarta, sau guda kōwace rānā.
Nā shaida yā Ubangijina, da kā halitto ni, don in san ka, kuma in yī maka sūjada. Nā tabbata a wannan lōkacin, kāsāwāta da iyāwarka, talaucīna da arzikinka.
Bābu wani Allah sai kai, mai cēto cikin matsala, mai rāyuwa cikin īkonsa.
Kana wanke hannuwa, ka cē :
Yā Allah, ka bā hannuwāna ƙarfi da īkon ɗaukar kitābinka; kada kōmi ya sā su falgaba. Kaucē su da shiga abinda bai shāfē su ba. A gaskiya, kai nē mai īko, ƙadīran.
Kana wanke fuska, ka cē :
Nā juya fuskāta wajenka, yā Ubangijina. Hanā ta da kula da kōmi bāyan kai, kuma ka haske ta da annurinka mai ni’ima.
Yā Allāna, Ubangijina! Nī bāwanka ne, kuma ɗan bāwanka. Nā bar mabartata tun assuba, a lōkacin da tarmāmuwar kaɗaitakarka take ɓullōwa a cikin yardarka, tana wātsa haskenta a sararin dūniya gabāɗaya, bisa umurnin da ka bāda a cikin littāfin ƙaddararka.
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allāna, a bisa abunda muka wāye mā na ɗaukakar hasken saninka. Ka saukar mana, yā Ubangiji, da abunda zā ya fadaƙar da mu, ya kauce mu da duk wani abun da bā kai nē ba, kuma ya kauce mu da duk wata dōgara in bā garēka ba. Ka tabbatar mā duk waɗanda nike ƙauna, yan uwāna maza da māta, da nī kaina, alhērin dūniya da na lāhira.
Yā kai abun ƙaunar duk halitta, abun sō ga duka dūniya, ka kēɓē mu a cikin ɗaukakarka, daga sharrin waɗanda ka la’anta, māsu raɗar ɓanna, a cikin zukācen mutāne. Kai nē mai īkon aikata abunda kake sō. Kai nē bā shakka, mabuwāyi, mai taimako cikin hallaka, rāyayyen sarki.
Yā Ubangijina Allah, ka saukar da alhēri bisa wanda ka hīhīta, wanda ta hanyarsa, ka wāre nagari da maƙētata, kuma ka taimakē mu cikin alhurmarka, don mu aikata abūbūwan da kake sō, kake ƙauna.
Yā Ubangijina, ka saukar da albarkarka bisa wanɗanda suke wanzama kalmarka, kuma da waɗanda suka jūya fuskarsu zuwa garēka, kuma suka saurāri kiranka. Hakīka, kai nē Ubangijin halittu, mai mallaƙar kōmi.
Shīnē mai yalwa, mai kyauta ! Yabo ya tabatta ga Allah, mai dawwama, maras sauyāwa, maras gōcēwa, mai rayuwa har abada, wanda zātinsa yake shaidar cēwa, haƙīƙan, Shī kaɗai yake, bā Shi abōkin tārayya, mai ƴanci, mafi girma ! A gaskiya, mun shaida cēwa, bābu wani Allah illa Shi, mun yarda da kaɗaitakarsa, kuma mun tabbata da ɗayantakarsa, bā wani Allah sai Shi. Har kullum, Yā wuce gaban a kai garēshi, girmanshi bā ya da iyāka, kuma yā fi ƙarfin kwatamci.
A lōkacin da Ya sō bayyana alfurmarsa da alhērinsa zuwa ga mutane, kuma dōmin Ya tsāra dūniya, sai ya sauko umurni, kuma ya kafa dōkōki. Cikin waɗannan dōkōki, akwai aure da Ya maida shi tamkar gārun jin dāɗin rāyuwa da tsīra, daga samāniyar tsarkakarsa, Yā rubuta wannan dōka cikin Littāfi Mafi Tsarki. Ya cē, ɗaukaka cē mai girma : « Ku yi aure dōmin ku haifi wanda zai tuna mani bāyūna. Wannan ɗaya nē daga cikin umurnīna, ku bī shi don jin dāɗin rāyuwarku ».
Ginshiƙin aure a cikin addinin baha’i shīnē, haɗin kai da shiri tsakānin ango da amarya. Amma, yā cancanta su yi hattara matuƙa, kuma su kōyi bin hanyar sanin jūna da kyau. Yā kamata wannan igiya wadda bā ta cirēwa, ta danganta bisa ma’āmala mai ƙwāri, dōmin shinfiɗa shiri, aminci da haɗin kai, sabōda kaiwa ga rāyuwar har abada.
Abdul’Baha
Kamar yanda Allah ya umurto cikin Kitābil Aƙdas (Littāfi Mafi Tsarƙi), dōmin a ɗaura auren, yā cancanta ango da amarya, su karanta wannan āyā gaban wakīlan majalasar tara :
Ango ya cē :
« A gaskiya mun dōgara ga nufin Ubangiji Allah »
Amarya ta cē :
« A gaskiya mun dōgara ga nufin Ubangiji Allah »
Shīnē Allah ! Yā Ubangiji mafi kwatamci ! Cikin basīrarka maras iyāka, kā umurci yan adam da yin aure, dōmin zūriyarsu ta bi mā jūna cikin wannan dūniya mai ƙārēwa, kuma har kullum, su rāyu cikin ibāda gaban fādar kaɗaitakarka, suna rōƙo da yabonka, cikin sūjada, da hamzarin bauta maka.
«Allah yā halitto rūhunnai da mutāne don su yabā shi»
Don haka, ka haɗa, cikin samāniyar rahamarka, waɗannan tsuntsāyen gidan ƙaunarka, kuma ka sā, su zauna wurin da alhumarka zā ta dinga saukōwa, ya zamanto daga haɗuwar waɗannan tēkun ƙauna, ƙōramar sōyayya ta halitto zūriya mai kiyāwon lu’ulu’u, da zā ta ɓullo ta fito hīli.
«Yā garwaya tēku biyu suna haɗuwa. A tsakāninsu, yā kurta iyāka da bai cancanta ba su ƙētare. Waɗanne daga cikin ni’imōmin Ubangijinku zā ku wātsar ? Ya nā fitar daga kōwannensu, lu’ulu’u manyā da ƙanānā.»
Yā kai Ubangiji mayalwaci ! Ka sā kyaukyāwar haifuwa ta sāmu daga wannan aure.
Kai nē bā shakka, mabuwāyi, mafi girma, mai gāfara da bā ta da iyāka.
Ta yāyā zan nēmi barci, yā Allah Ubangijina, alhāli kuwa, ina ganin wanɗanda suke ƙaunar ka, bā su rumtsāwa don tsananin tsōron su yi nēsa da kai, kuma, ta yāyā zan mīƙē, in nēmi hūtū a kan gā shi ina ganin rāyukan māsu ƙaunar ka, suna kūkan sun yi nēsa da kai?
Yā Ubangijina, nā damƙa rūhūna da duka gabāɗayāna a hannun dāmar ƙudurarka da kāriyarka. A cikin sō da yardarka nē, idan na kwanta nike aje kaina, kuma nike ɗagā shi.
A gaskiya, kai nē mai kārēwa, wanda yake tsaye bisa kōmi, mabuwāyi, ƙadīran. Ina barci, kō ina falke da īkonka, bā wani abun buƙātāta, illā abin da kake so. Nī bāwanka ne, ina cikin hannuwanka. Ka taimakē ni cikin rahamarka, in aikata abūbūwan da zā su baza ƙamshin ƙaunarka.
Bā shakka, da ni da duk wanɗanda suke ƙaunar ka, gūrinmu kēnan. Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangijin tālikai.
Yā Allāna, majibincīna, maƙārashin duk wata bukātāta ! Gā bāwanka nan yana niyyar ya rumtsa a cikin inuwar rahamarka, yā kwanta ƙalƙashin samāniyar alfurmarka, yana rōƙon umurninka da tsarinka.
Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, da idonka wanda bā ya rumtsāwa, ka hana idānuwāna dūbin wani abu, in bā kai ba. Ka ƙarfafa ganīna, ta yanda zan tsinkāyi alāmunka, kuma in yi shāwar kallon wahayinka. Kai nē wanda tabbatar ƙadīrarka ta gētse duka tūshen mulki.
Bābu wani Allah illā kai, mabuwāyi, mai nasara, marar iyāka.
Yā Ubangiji, nā jūya huskāta wajen fādar ɗayantakarka, kuma nā nutsa kaina cikin tēkun rahamarka. Yā Ubangiji, ka wāye idānuwāna cikin wannan duhun, don tsinkāyen haskenka mai cikakken haskēwa, ka mayar da ni maji dāɗi a wannan zāmani mai abun al’ajabi ta wajen ɗanɗanon ƙaunarka.
Yā Ubangijina, ka sā in ji kiranka, ka kuma būɗe mani ƙōfōfin arshinka, dōmin in ga annurin ɗaukakarka, ta yanda zā ta huzgē ni zuwa wajenka.
Lalle, kai nē mai bayyanarwa, karīmin, mai rahama, mai yāfēwa.
Yā Allah, ka sanyaya, kuma ka farinta rūhuna. Tsarkaka zūciyāta. Haskaka hankalīna. Nā damƙa dukan al’amurāna cikin hannunka. Kai nē shūgabāna da maɓūyata. Bā nā son zama cikin baƙin rai da hushi. Nā fi son zama cikin farin ciki da murna.
Yā Ubangijina, bā ni son zato da azāba su māmāye ni.
Yā Allah, ka fi sō nā, da yadda nike son kaina. Nā dawwama garēka, yā Ubangijina.
Baha’u’llah
Yā Allah! Yā Allāna! Gā bāwanka nā nufa wajenka, kuma da zūciya guda, yana rātsa hamādar ƙaunarka, kan hanyar bauta maka, cikin jiran taimakonka, bisa ga tsammānin yalwarka, amince da īkonka, kuma tāre da ni’imarka.
Yā Allāna! Ka sā ƙaunar bāwan nan nāka a garēka, ta ƙāra fīfīta, kullum, kada ya daina yabā ka, kuma hamzarinshi wajen ƙaunarka, ya ƙāra cī gaba. Hakīka! Kai nē mai saukar da ni’ima, yalwarka bā ta da iyāka.
Bā wani Allah sai kai, mai jinƙai, mai rahama.
Ka ƙirƙiro mani zūciya mai tsarki yā Allāna, kuma ka tabbatar mani da kyaukyāwan lamiri. Yā abun bēgēna, a cikin ƙudurarka, ka ƙarfafā ni bisa hanyarka, yā abun ƙaunata. Ka sā hasken ɗaukakarka ya būɗe mani hanyā zuwa garēka.
Yā kai mafārin duk bukātūna. A cikin girmanka mabuwāyi, ka ɗaukaka ni a samāniyar tsarkakēwarka, yā kai mafārin fāruwāta, ina rōƙon ka, a cikin zamancēwarka marar iyāka, ka sā in rāyu cikin farin ciki, yā kai da kake Allāna. Ka saukō mani kwanciyar hankali, yā kai abōkin zamāna, ka sā annurin fuskarka ya kai ni nēsa da duk wani abu in bā kai ba, yā Ubangijina, ka sā lābārin tabbatarka da ɗayantakarka, su cika zūciyāta da murna. Yā kai mai girma, ayyananne, wanda ya tabbata gaba da kōmi, kai nē mai cikakken sirran cikin ban māmāki.
Yā Ubangijina ! Ka sā kyaukyāwar alāmarka ta zamanto abuncīna, kusancinka abun shāna, ƙaunarka gūrina, yabonka abun aikatāwāta, tunāninka abōkin tafiyāta, ƙudurarka kāriyāta, wurinka mabartāta, kuma ka sā gidāna ya zama wurin da ka shāre duk wasu abūbūwan da suka tsayar waɗanda yāna ta kāre su da kai.
A gaskiya kai nē mabuwāyi, jalla babban sarki, ƙadīran.
Dukan yabo ya tabbata a garēka yā Ubangiji Allāna ! Ina rōƙon ka, da sūnanka mai martaba da aka tsare cikin kurkukun birnin Akka, wanda ya fāɗā hannun maƙiyansa, kuma la’anannu suka zāre masa takubbansu, ka bā ni ƙarfin da zan zama tsayayye cikin addininsa, kuma in jūya kallōna wajensa, ta yanda bā wanda ya isa ya karkatar da ni.
Nā shaida yā Ubangijina cēwa, yā bāyar da ransa bisa hanyarka, kuma don tsananin ƙaunarka, yā gwammace da wahala. Bābu cin mutuncin da ba a masa ba, don yā bayyanar da mulkinka zuwa ga bāyunka, kuma yā ɗaukaka kalmarka gaban halittarka. Kō da yake, matsalōli suna ƙāra cī gaba, kuma darūrar da ka zubo masa tā māmāye shi ta kō’ina, sai ya ƙarfafa cikin tunāninka, har ya zamanto duk yawan waɗanda suka wātsar da alāmunka, kuma su ka ƙi bāda gaskiya a garēka, sun daina bā shi tsōro.
Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, a bisa darajarsa da duk abunda yake nāsa nē, ka sā ƙaunāta ta tabbata a garēshi, kamar yanda ƙaunarsa ta tabbata a garēka.
Nā shaida da cēwa, ƙaunarsa ƙaunarka cē, bayyanarsa bayyanarka ce, haskensa haskenka nē, kuma addininsa addininka ne.
Kada ka hana mani yā Ubangijina, abun da ka mallaka, kada ka dāmu don nā mance abun da kake sō a rānēkunka. Hakīka, kai nē mabuwāyi, maɗaukakin sarki, jalla mafi basīra.
Igiyar dake ɗaure zūkāce yanda ya kamāta, ita cē, biyayya. Idan sun haɗu, yā cancanta masōyā, su gwadāwa jūna amānā matuƙa.
Kada ku yarda kīshi, ya shiga tsakāninku, sabōda kīshi, kamar gubā, yana gurɓāta tūshen sōyayya.
Kada ku yarda, matsalōlin yau da kullun, da hālin zaman yau da gōbe dake sauyāwa kōwace rānā, su zama dalīlin rabuwarku.
Idan tāshin hankali ya ɓullo, ku tattauna tsakāninku, sabōda tsōron kada waɗansu, su maida ƙwāyar ƙasa ta zama babban dūtsi.
Zūkācenku, su zama kamar madūbai biyu, dake gwada ƙyalƙyalin taurārun samāniyar sōyayya da shāwa.
Martabarku da īmāninku, su zama sū nē abun zancenku. Kada ku ɓōyēwa jūna kōmi. Gidanku, ya zama mafaƙar hūtū da konciyar hankali.
Ku karɓi kōwā. Ku būde ƙōfarku ga aminnai kō ɓāki. Ku karɓi maziyartanku da marhaba cikin shinfiɗar huska. Duk wanda ya zō gidanku, ya jī kamar yā zō gidansa nē.
Gidanku, ya zama tamkar aljanna, duk wanda ya shiga, ya ga tūshen ƙāyatarwa, kuma ya yi kirārin cēwa, « gā gidan sōyayya ! Gā fādar sōyayya ! gā gidan tsuntsāyen sōyayya ! gā garkar sōyayya!»
Idan Allah Subahānahu wa ta āla ya bā ku yāra nagari, ku ɗauki nauyin bā su tarbiyya, kuma ku jāgōrancē su, har su zamana furanni da bā su yaushi, cikin lambun wardin Ubangiji, su zama tsuntsāyen aljanna, su zama māsu kyautatāwa al’umma, a taƙaice dai, su zama sū nē ƴāƴan itāciyar rāyuwarku.
Ku zamēwa jūna, tamkar masōyan samāniya, kuma gātāyen Ubangiji, dake zaune cikin aljannar sōyayya.
Ku gina mabartarku bisa rēshen iccen sōyayya.
Ku yi tafiya cikin garkar wardi maras ƙārēwa ta sōyayya.
Ku tsaya tsayin daka, bisa hanyar sōyayya.
Ku shinshina ƙamshin furannin sōyayya.
Gūrinku, ya ƙunshi karāmar abincin sōyayya, kuma batūtuwanku, su zama tamkar jērin farāren lu’u’lu’un tēkun sōyayya.
Ku shā matuƙa, ruwan sōyayya, sabōda ku rāyu har kullun cikin ƙaunar Allah Ubangiji.
Ya jalla, Ubangiji Allāna ! Ina maka gōdiya da ka sā a cikin yardarka, na bāda gaskiya da tabbatarka, ka kubtar da ni daga cikin maƙiyanka, ka būɗe idānūna har na gāne da mummūnan abūbūwan da suke aikatāwa, ka kēɓē ni da duk wata rātaya da su, ka sā na maida duk al’amurrāna zuwa ga alhurmarka da karāmarka.
Ina maka gōdiya, yā Ubangijina, da ka saukar mani daga gizāgizan yardarka, abūbūwan da suka kāre ni da habaicin kāfirai, kuma da ba’ar la’anannu, ka sā na kafa zūciyāta zuwa tunāninka, ka sā na yi nēsa da waɗanda suka ƙi gānēwa da hasken huskarka.
Ina kuma gōdiya, da ka bā ni dāmar in kasance tsayayye cikin ƙaunarka, in yi yabonka, in ɗaukaka sūnanka. Ina maka gōdiya, da ka ƙōsar da ni da ruwan rahama, wanda darajarsu, ta haye duk wasu abūbūwan da suka bayyana, kō suke ɓōye.
Kai nē Jalla, mafi ɗaukaka, mai cikakkar ƙauna.
Yā Allāna ! Yā Allāna !
Haɗa zukācen bāyinka, kuma ka bayyana musu nufinka mai girma. Dā dai su bi umurninka, kuma su kiyāye dōkōkinka ! Taimakar su, yā Allāna, a cikin ƙōƙarinsu, kuma ka bā su ƙarfin bautā maka.
Yā Allāna, kada ka daina tafiyar da su, amma, daga annurin saninka, ka raka sāwunsu, kuma cikin ƙaunarka, dāɗaɗa rāyukansu. Kai nē mataimakinsu, kuma Ubangijinsu.
Ɗaukaka nā garēka, yā Allāna, kuma yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangijina ! Da sūnanka mai gwada īkonka da ƙarfinka, ina rōƙon ka tsarkake madūban zūkacen bāyinka da dauɗar shakka da zato, kuma ka tafiyar da ɓatattu wajen haskenka, don su gāne da kaɗaitakarka, kuma su bāda gaskiya, da kai kadai kake. Yā Allāna, tsīra ta tabbata a garēka, kuma bā wata hanya in bā ta fādarka ba. Lōkacin da al’umarka ta hōru da saninka, yā Allāna, bā zā ta kēɓē daga hanyarka ba. Taimaki wannan al’umma, ta tsaya daidai cikin umurninka, a lōkacin da take nufa wajenka, don ta sāmu isā fādarka, kuma ta cika irādarka. Kai nē mai matuƙar girma da rahama.
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allāna! Kai nē wanda daga būɗa bāki, sai duka dūniya ta yi gilgiza, wanda daga kurta alƙalaminka, ka rarraba bāyunka. Nā shaida yā Allāna, da cēwa, a wannan wahayi, kalmarka guda ɗaya tā sā duk halitta tā zama mai hallaka, kuma da wata kalmar, duk wanɗanda ka zāɓā, suka rāyu da sābuwar rāyuwa, dōmin alfurmarka da karāmarka. Sabōda haka, nike maka gōdiya da yabo, don darajar duk waɗanda kake ƙauna, waɗanda ka sāke rāyāwa da ruwa māsu rāyarwa, da suka ɓullo daga marmaron yardarka.
Tunda yake, kā rāyar da su a cikin alhērinka mai girma, yā Allāna, ka sā hankalinsu ya kōma zuwa wajen umurninka. Da yake kā yarde musu, shiga cikin ɗākin addīninka, ka yarde musu a cikin alfurmarka, kada kōmi, ya riƙe su nēsa da kai. Ka būɗe mā zukācensu yā Allāna, ƙōfōfin saninka, don su gāne da kai nē wanda ya fi a gāne shi, wanda duk halitta ba ta isa ta farga da iyākacinsa ba, wanda yake yā wuce inda, kōmin ƙōƙarin bāyinka, su fahimta da yanda kake ciki, kuma ka wanke zukācensu, dōmin kada su kula da waɗannen maƙaryata, māsu yawan sūrūtu da suke ƙariyar batu da sūnanka.
Yā Ubangijina, ka bā bāyin nan nāka, hamzarin da zā su sarkafa a addīninka da kuzāri ta yanda har abada, bā zā su kula ba da habaicin wanɗanda ba su sā kōmi gaba ba, in bā abun dūniya ba, masu aikata abūbūwan da ka hana a cikin litattafanka da kitābanka. Kā san yā Allāna, ina jin kūkan kūrāyen da suke bayyana da kamannin bāyinka. Ka kāre masōyanka da sharrinsu, kuma ka yarda su riƙe abin da ka bayyana cikin wanan wahayi nāka wanda cikin saninka, ka ƙayyada cēwa, bā shi abōkin tārayya.
Ka isar musu, yā Allāna, da abun cin mōriya, ka haske su da hasken saninka don su fahimta da kai nē sama ga kōmi, kuma su shaida da ɗaukakarka a bisa halittarka da nasararka ga waɗanda suke sama da na ƙasa. Ka na da īkon aikata kōmi, yanda ka ga dāma. Bābu wani Allah in ba kai ba. Kai nē jalla, wanda duk tāliki yake rōƙon taimakonka.
Yabo ya tabbata a garēka, yā kai Ubangijin tālikai.
Yā Allāna, zukāce da yawa masu sanyi, sun zāzāfa kusa da gumin addīninka. Hankulla da yawa masu gyangyaɗi, sun wartsake da suka ji zāƙin muryarka. Sabbin zuwa da yawa, sun nēmi mafaƙa a ƙalƙashin ɗayantakarka. Ma jī ƙishirwa da yawa, sun nēmi ɗanɗana ruwan rījiyarka mai rāyarwa, a wannan rānar rānaikunka!
Alhēri ya tabbata, ga wanda ya juya fuskarshi wajenka, kuma ya gaugauta, don ya iske tarmamuwar sāhiyar hasken huskarka.
Alhēri ya tabbata, ga wanda a bisa hanyarka ya ɓatar duk dūkiyar da ka mallakar masa a cikin kyautarka ta wajen taimako.
Alhēri ya tabbata, ga wanda don tsananin ƙaunar ka, ya yi wātsi da duk wani abu da bā kai nē ba.
Alhēri ya tabbata, ga wanda dōmin murnar sāduwa da kai, ya rabu da sarkafa da kōmi in ba kai ba.
Ina rōƙon ka, yā Allāna, da wanda shīnē sūnanka, kuma cikin īkonka, ya tāshi sama daga kurkukun da yake ciki, ka ƙaddarāwa kōwa, abun da kake sō.
A gaskiya, ƙudurarka ta wuce gwalgwado da kōmi.
Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangiji Allāna. Ga bāwanka, wanda a cikin hannunka, ya shā ruwan rahamarka, kuma ya ɗanɗana dāɗin ƙaunarka a wannan rānā wadda take tāka.
Ina rōƙon ka, don darajar bayyana sunāyenka, ka kāre shi da duk wata darūra da zā ta hana shi ƙaunar ka, kō ta kaudar da fuskarshi daga kallonka; ka kāre shi, ta yanda randunōnin māsu sakaci su kāsa kaucar da shi daga hanyar jin dāɗinka. Ina rōƙon ka bā shi arzikinka, kuma ka ɗaukakā shi yanda zā ya hangi dūniya, ya gāne da abu cē mai wucēwa kamar ƙibtar ido. A cikin īkonka marar iyāka, ka kāre shi da duk abun da kake ƙyāma.
A gaskiya, kai nē Ubangijinsa, kuma Ubangijin duka tālikai.
Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangiji Allāna! Gā ni ina nēman tarbon irādarka, kuma nā nufā wajen kujērar alfurmarka. Nī nē wanda na yi wātsi da kōmi, na nufi ƙalƙashin kāriyarka, na jūya fuskāta wajen munbārin bayyanarka da zauren ɗaukakarka.
Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, don kiranka wanda ya sā waɗanda suka bāda gaskiya ga ɗayantakarka, kuma suka zābura nēman tsīra ƙalƙashin rahamarka, kiranka da ya sā māsu ciki ɗaya, suka yi nēsa da kansu, kuma suka yō wajen sūnanka mai girma, wanda ta wajenshi āyōyinka suka sauko, alkawalinka ya cika, shaidarka ta tabbata, haskenka ya bayyana, gaskiyarka ta tabbata, alāmunka ya huto hīli.
Ina rōƙon ka sā ni cikin waɗanda ka ƙilga da su, shan ruwan hannuwanka, ruwa māsu rāyarwa da rāyuwa ta gaske, ka kuma sā ni cikin waɗanda suka yi wātsi da kōmi nāsu, kuma suka nufi wurinka, waɗanda suka wadāta da baiwarka marar iyāka, kuma lēɓunansu nā riƙe da yabonka, zukācensu ɗauke da tunāninka, suka gaugauta zuwa ga hīlin shuhāda.
Ina rōƙon ka, yā Allāna! Ka saukar mani da abunda zai rabā ni da duk wani abun da bā kai nē ba, kuma ka kāre ni daga sharrin maƙiyanka waɗanda suka ƙi bāda gaskiya ga alāmunka. Kana da īkon aikata abunda kake sō.
Bābu wani Allah illa kai, mai taimako cikin hallaka, mai rāya kansa da kansa.
Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangiji Allāna, nī nē bāwanka wanda ya sarƙahu ga igiyar rahamarka. Ina rōƙon ka, da sūnanka wanda ya mallaƙi kōmi, a cikin waɗanda ake gani da na ɓōye, sūnanka wanda daga shīnē, rāyuwar gaskiya ta bayyana bisa kōmi da kōwa. Ka ƙarfafā ni a cikin mulkinka wanda ya wanzama sama da ƙasa, kuma ka kāre ni da duk wata cūta kō wahala.
Nā shaida cēwa, kai nē Ubangjijin duka sūnāye, mai yancin umurtar duk abun da yake gani daidai nē a garēshi. Bābu wani Allah illa kai, mabuwāyi, masanin duk abun dake ɓōye, mai basīra.
Ka ƙaddaro mani, yā Ubangijina, abun da zai zama mai alhēri nē a garēni dūniya da lāhira. Ka sā ni cikin alkawarin da ka mā zāɓaɓɓun bāyunka, waɗanda ban tsōron munāfikai, tankiyar kāfirai kō duhun ran waɗanda suka nīsanta da kai, ba su hanā su ba jūyāwa zuwa garēka.
A gaskiya, kai nē mai taimako cikin hallaka da girman mulkinka. Bābu wani Allah in bā kai ba, maɗaukaki, mabuwāyi.
Ka cē: Yā Allah, Ubangijina, kai kā bā ni wannan ajjiya, kuma cikin irādarka, kā kirāyē ta wanjenka. Nī da nike baiwarka, bā ni da īkon cēwa: «yāyā aka yi haka, kō mī ya sā haka? » Alhāli kai nē abun yabo, kuma yā cancanta a karɓī duk abūbūwan da ka aikata, kō ka ƙaddara.
Yā Ubangijina, baiwarka tā damƙa fātarta ga alfarmarka da alhērinka. Ka ƙayyada mata abun da zai kusantō ta wurinka, kuma da zā ta ci mōriyarsa dūniya da lāhira. Kai nē mai jin-ƙai, Alkarīmu. Bābu wani Allah illā kai, mai ƙudura, mai ɗōrēwa kōwace rānā.
Yā Allāna! Yā kai mai gafarta zunubi, mai saukar da ni’ima, mai kaudar da matsalōli. Lalle nē, ina rōƙon jin-ƙanka, ga waɗanda suka huta daga gangar jikinsu, kuma su ka nufi samāniya wajen makōmar rūhu.
Yā Ubangijina, gāfartā musu kuskurensu, kēɓē musu azāba, kuma ka sā duhun da suke ciki, ya zama haskē. Būɗē musu ƙōfar wadāta, tsarkakē su da ruwa mafi tsarki, kuma ka yardē musu tsinkāyar īkonka daga birji mafi ɗaukaka.
Wā bāya ga Allah kē kauda matsalōli ?
Cē : Yabo ya tabbata ga Allah, shī kaɗai nē Ubangiji, kōwa bāwa nē a garēshi, kuma kōmi nā ƙalƙashin īkonsa.
Tabbatā cēwa : Allah yā wadāta ga kōmi, ya hiye ga kōmi. ƙasa da sama, bāya ga Allah, bā abunda kē dācēwa halitta. Hakīka, Ubangiji, shīnē masani, madawwami, mai mallaƙar kōmi.
Sūnanka warkarwātā nē, yā Ubangijina, kuma tunāninka māgāni nē a garēni. Kusanci da kai nē bēgē na. Ƙaunarka ita cē abōkiyar tafiyāta. Rahamarka, ita cē warkēwāta, da madōgarāta dūniya da lāhira.
Bā shakka, kai nē mayalwaci, masani, mafi basīra.
Yā Allah, Ubangijina, ina rōƙon ka, a cikin tēkun warkarwarka, da hasken tarmāmuwar sāhiyar alhurmarka, da sūnanka wanda yake abun yabo ga bāyunka, da hazāƙar maganarka, da girman alhurmarka, kuma da rahamarka tabbatacciya tun kāfin abūbūwan da suke sama da ƙasa su tabbata, ka tsarkake ni da tsarkakakkun ruwan nan nāka waɗanda suke cike da rahamarka, ka kāre ni da kuskure, kāsāwa, tāshin hankali kō duk wani shirme.
Yā Ubangijina, kana ganin bāwanka nā rōƙō a ƙōfar alhērinka, sarƙafe ga igiyar karāmarka, yā maida duk gūrinsa a garēka.
Ina rōƙon ka yā Allāna, kar ka hana masa abunda ya rōƙe ka cikin dubun alhurmarka da hasken tarmāmuwar kyautatāwarka. Kai nē mai aikata abunda kake sō. Bā wani Allah illā kai, mai gāfartāwa, mayalwaci, karīmi.
Yā Ubangiji Allah maɗaukakin Sarki ! Ina rōƙon ka da sūnanka wanda ta garēshi ka ɗōra wanda shīnē kyāwonka, bisa kujērar īkon addīninka, sūnanka wanda da shīnē, kake sauyā kōmi, kuma kake haɗa kōmi, sūnanka dake hukunta kōmi, kake sallamar kōmi, kake kāre kōmi.
Ina rōƙon ka kāre baiwarka wadda ta nēmi ɓūya garēka, kuma take nēman kāriyar wanda garēshi ka bayyana. Wannan baiwar tā mīƙa duka gūrinta da amincinta a garēka. Bā ta da lāfiya yā Allāna! Amma tā shiga ƙalƙashin inuwar iccen warkarwarka. Tā furgita, sai ta tsēro cikin birnin taimakonka, cūta tā kāda ta, sai ta nēmi ɗugon ruwan rangwamenka, tā tsōrata, sai ta zābura don ta iske ƙōramar kwanciyar hankalinka, tā ɗau zunubi, sai ta maida fuskarta wajen dakalin gāfararka. Ka rufēta a cikin īkonka, da mayāfin warkarwarka da alhurmarka, yā Allāna, abun ƙaunāta! Ka kōri ƙishirwarta da kāriyar rahamarka da ni’imarka. Ka kāre mata duk wata azāba, matsala kō cūta, kuma da duk wani abun da yake la’ananne a ganinka.
A gaskiya, kai nē wanda ka fi ɗaukaka bisa ga kōmi in ba kai da kanka ba. Hakīka, kai nē mai warkarwa, wanda ya isa ga kōmi, mai kārēwa, mai jin-ƙai har abada, mai rahama.
Yā Allāna, kai nē, wanda sūnayenka kē warkar da māsu cūta, kē sauko lāfiya ga masākai, kē ƙōsar da māsu ƙishurwa, kē kwantar da hankalin firgitattu, kē jāgōrar ɓatattu, kē ɗaukaka wanɗanda aka ƙasƙanta, kē arzita matalauta, kē wāyar da kan jāhilai, kē haskaka zukācen māsu duhun rai, kē sā murna ga māsu hushi, kē sā kuzāri ga zukācen da suka yi sanyi, kē karɓo hakin waɗanda aka zālunta.
Da sūnanka nē yā Allāna, duk halittu suka rāyu, samāniya ta warware, ka halicci ƙasa, gizāgizai suke shāwāgi, ruwan sama suke zubōwa.
A gaskiya, duka wannan abūbūwa suna tabbatar da alhurmarka ga duka halitta. Don haka nē nike rōƙonka, da sūnanka wanda da shīnē ka bayyana ɗayantakarka, kuma ka ɗaukaka addininka sama ga duka halitta gabāɗaya, dōmin sūnāyenka mafi ɗaukaka, dōmin zātinka da ya fi ƙarfin yabo, ka sā a daren yau, daga gizāgizan rahamarka, ka sauko da ruwan warkarwā bisa wannan ɗan jārīrin da ka rāɓā garēka, cikin dūniyar da ka halitta.
Yā Allāna, ka sā masa rīgar lāfiya da rāyuwa, yā abun ƙaunāta, ka kiyāye masa duk wata darūra kō cīwo, kuma ka kauce shi da duk abunda ka la’anta.
A gaskiya, mulkinka kē daidaita kōmi, kai nē karīmin wanda kē rāyuwa da kansa. Kuma ka tabbatar masa yā Allāna, da alhērin dūniya da na lāhira. Ƙudurarka da basīrarka sun isa ka aikata haka.
Yā kai wanda matsala daga garēka ita cē cikakken māgani ga waɗanda suke kusa da kai, wanda takōbinka, abun ƙauna nē ga waɗanda suke son ka, wanda zūkācen māsu ƙaunarka, bā su jiran kōmi a garēka, in bā sūka ba, kuma ƙadararka ita cē abun bēgen waɗanda suka bāda gaskiya a garēka.
A cikin rangwamenka da girman ɗaukakar huskarka, ina rōƙon ka sauko mana, da abunda zā ya sā mu malmatso kusa da kai. Ka daidaita tākinmu cikin addininka, yā Allāna, ka haskaka rāyukanmu da hasken cikakken saninka, ka wāye zukātanmu da hasken sūnāyenka.
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allāna ! Nā nēmi shaida ga īkonka, in bā don wahala da azābar da suke daurēwa cikin bin hanyarka ba, yāyā zā a gāne da wanɗanda suke cikakkun māsu ƙaunar ka ? Yāyā zā a bambamta matsayin masōyanka da sauran ? Māsu ƙaunarka, bā su da waɗansu abukkai in bā hawāyensu ba, māsu biɗarka, bā su da waɗansu mahakurta, in bā kūkansu ba, māsu gaugautāwa zuwa garēka, bā su da wani abinci, in bā nāman zūciyarsu ba da ta ciccire.
Duk wani baƙin cikin da zai sāme ni a hanyarka, abun murna nē a garēni. Duk wasu kibban maƙiya, da zā su kafu māni don ɗaga kalmarka, abun shāwa nē a garēni. Ka bar ni, in shā cikin addininka, yā Allāna, duk abūbūwan da ka sō ni da su, kuma ka aīko mani abun da ka ƙaddaro cikin ƙaunarka.
Yā jalla ! Bā nā ƙaunar kōmi, sai abun da kake ƙauna, kuma bā ni shāwar kōmi, sai abun da kake shāwa. Nā dawwama a garēka har kullum. Ina rōƙon ka yā Allāna, ka ɗaukaka waɗanda suka bāda gaskiya ga wannan bayyanar tāka, waɗanda suka cancanta da sūnanka, kuma da mulkinka don su sāmu dāmar tunāwa da ni cikin halittarka, kuma su ɗaga garkuwar nasararka.
Kana iya aikata duk abun da kake sō. Bābu wani Allah illā kai, mai taimako cikin hallaka, mai rāya kanshi da kanshi.
Yā Allah Ubangijina, kar ka kasance nēsa da ni, sabōda matsalōli sun māmāye ni. Yā Allah Ubangijina, kar ka bar ni in cēci kaina da kaina, alhāli ƙiyayya mai tsanani tā hayyacē ni. Ka ƙōsar da ni da tātāccen nōnon karāmarka, sabōda ƙishurwa tā kāma ni matuƙa. A ƙalƙashin fufuken rahamarka, ka kāre ni sabōda maƙiyāna sun haɗu sun zāburo mani gabāɗayansu. Tsare ni kusan gadon mulkinka, gaban alāmu māsu nūna dawwamarka har abada, sabōda ƙarfīna yā ƙāre. Da luddan ruwan murna da hannun rahamarka ya mīko, ka haƙurar da ni, sabōda baƙin ciki mai nauyi yā tsananta mani. Ka rufe ni da rīga mai zubin cikakken īkonka, sabōda talauci ya yāce ni gabāɗayāna. Ka yarda in hūta cikin saurāren tāwan kūkan kurciyar samāniyarka, sabōda baƙar darūra tā rufe ni.
A gaban gadon ɗayantakarka da hasken kyaukyawar huskarka, ka sā in tsaya, sabōda tsōro da karkarwa sun hallaka ni. A cikin kōgin rangwamenka nike sō ka zundumā ni, sabōda yawan zunubbaina sun ɓatar da ni gabāɗayāna.
Yabo da ɗaukaka su tabbata a garēka yā Allāna. Ina rōƙon ka, don darajar shaidar māsu ƙaunarka, da hawāyen waɗanda suke tsananin buƙātar ganin ka, kar ka hana mani rahamarka a wannan babbar rānā tāka, kuma kar ka hana ni jin kūkan tantabarar nan mai wāka ɗayantakarka a gaban hasken huskarka.
Kana gani nā cikin tsananin talauci yā Ubangijina ! Gā shi nā sarkafa ga sūnanka mai mallaƙar kōmi. Nā san kat, da ina hallaka, sai gāshi nā sarkahu ga sūnanka wanda ya fi gaban hallaka. Don haka nē, nike rōƙon ka, don zātinka mai martaba, maɗaukaki, kar ka bar ni in fāɗa cikin miyāgun ayyuka. Ka riƙe hannūna cikin hannunka mai ƙarfi, ka zāgo ni daga cikin zurfin ra’ayīna karkatacce, ka hudda mani duk wani tunānīna na wōfi, kuma ka tsarkake ni da duk abun da ka yi wātsi da shi. Ka bā ni ƴancin jūyāwā gabāɗayāna wajenka, in amince da kai, in yi gudu wajenka nēman ɓūya, kuma in zābura zuwa gaban huskarka. Kai nē, hakīka, wanda kake aikata abun da kake sō don girman īkonka, kuma cikin girman īkonka, kuma haka cikin girman mulkinka kake umurtar abin da ka ga dāma. Bā wanda ya iya tsayāwa gaban ƙaddararka, bābu wanda zai iya kēwaye nufinka. Gaskiya, kai nē ƙadiran, maɗaukaki mayalwaci.
Nā tāshi wannan sāhiya cikin alhērinka yā Allah. Nā huta daga gida, cikin cēto da dōgara garēka. Ka sauko mini albarka daga samāniyar jin-ƙanka. Ka kuma maida ni gida lāfiya, kamar yadda ka bā ni uzunin huta cikin kiyāyēwarka.
Bā wani Allah sai kai, kai kaɗai kake, mafi kwatamci, mai sani da basīra.
Nā falka cikin mafalkarka, yā Allāna. Yā kamaci duk mai nēman wannan wurin cēto, ya zauna cikin ɗākin ibādarka, kuma cikin tasmahar kāriyarka.
Yā Allāna, ka haskaka rūhuna da kyaukyāwar wallaharka, kamar yanda ka haske jikīna, da hasken sāhiyar ni’imarka.
Girmā ya tabbata a garēka, yā Ubangijina Allah, ina tambayar ka, a cikin darajar sūnanka wanda yake sama da duk sūnāye, wanda don girmansa samāniya ta tsāge, tarmamuwar sāfiyar haskenka ta bayyana cikakken hasken sūnanka maɗaukaki, managarci. Allah, ina rōƙon ka sauko mani da taimakon nan nāka mafi gwalgwado, kuma ka kāre ni, da kāriyar nan tāka nagartata. Ina ɗaya daga cikin bāyinka, yā mahaliccina, nā maida kaina zuwa garēka, kuma nā bāda yardāta a garēka. Ka tabbatar da ni, in zama cikin māsu ƙaunar ka, kuma ka lissāfā ni cikin māsu bin umurninka ta yanda kōmin hamzarin maƙiyanka, bā zā su iya rabā ni da kusantaka da kai ba. Ka tsarkaka kunnuwāna, yā Ubangijina, don in ji āyōyin da ka sauko, ka haskaka zūciyāta da hasken fahimta, kuma ka warware halshēna ta yanda zā ya iya wāƙa sūnanka. A cikin hukumcinka, yā Allāna, raina bai rātayu ga kōwa ba, in ba kai ba, zūciyāta kuma bā tā biɗar kōwa, in bā kai ba.
Bā shakka, bā wani Allah sai kai, jalla mayalwaci, mai gāfartāwa, mai jin-ƙai.
Daukaka ta tabbata a garēka yā Ubangiji Allah! Ina rōƙon ka ɗaga gizāgizan cikakkiyar rahamarka, ka zubo ruwan da zai wanke zukācen bāyinka da duka dauɗar da zā ta kāre huskarsu da dūbin wajenka, dōmin dukan gabāɗayansu, su bāda gaskiya a garēka, kai da ka rāyā su, ka halicce su. Ka taimake su yā Allah! Ta wajen girman īkonka, su sāmu dāmar shiga cikin hālin da zā su iya bambanta ƙamshin turāren tufāfin wanda ka ɗaukakā da sūnanka, maɗaukaki, don su sāmu dāmar ƙaunar ka, kuma su ɗanɗana dāɗin sāduwa da kai, ta yanda, kō dā zā su sāmu duka dūkiyar da kē sama da ƙasa, bā zā su daina yabon ka ba, kō su daina ɗaukaka sūnanka.
Yā abun ƙaunāta! Wanda raina ya fi sō, ina rōƙon ka, nī bāwanka wanda yake nēman fuskarshi ta sādu da tāka, ka kāre shi da waɗanda ba su bāda gaskiya ba garēka. Ka kāre shi da sūkar māshin waɗanda suka yi wātsi da sāƙonka. Ka sā wannan bāwa, ya bi umurninka, ya ɗaukaka sūnanka, ya maida hankalinsa wajen abun da ka sauko. Hakika, kai nē wanda har abada, ba ka taɓa kōre daga ƙōfar rahamarka ba, duk waɗanda suka dōgara garēka, kuma ba ka hana duk mai nufa wajenka ba, ya iso fādar karāmarka, bā wani Allah sai kai, maɗaukakin sarki, ƙadiran mabuwāyi jalla, marar iyāka.
Yabo ya tabbata ga sūnanka, yā Allāna, Ubangijin kōwa da kōmi, madōgarāta, madōgarar kōwa da kōmi, abin ƙaunāta, abun ƙaunar kōwa da kōmi, ƙarfīna, ƙarfin kōwa da kōmi, sarkīna, sarkin kōwa da kōmi, mamallakīna, mamallakin kōwa da kōmi, maƙārashīna, ƙarshen kōwa da kōmi, kai nē mai faɗaƙar da ni, mai faɗaƙar da kōwa da kōmi. Ina rōƙon ka yā Allah, kada ka amince da in yi nīsa da tēkun rahamarka, ka kiyāye ni da abun da zai nīsanta ni da gēfenka.
Bā wani abun da zai amfānē ni illa kai, yā Allāna, duk wata rāyuwa in bā kusa da kai ba, bā ta da wani amfani a garēni. Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, a cikin yawan arzikinka wanda ya maidā ka ba ka dōgara da kōwa ba sai da kai kanka, ka sā ni cikin waɗanda suka jūya fuskarsu wajenka, kuma suka tāshi tsaye, suna bauta maka.
Yā Ubangijina, ka yāfēwa bāyinka mazā da māta. Kai nē a gaskiya, mai gāfartāwa kullum, mai jin-ƙai.
Yā Ubangiji! Yā kai madōgarin tālikai! Kai nē matsirar duka bāyinka. Kai ka san asīrai da gaibu. Mū duka mun yi aikin zunubi, amma kai nē mai tsīrar da mazunubinta, mai rahama, mai jin-ƙai.
Yā Ubangiji, kada ka kula da kāsāwarmu. Ka dūbē mu da idon alhurmarka, da isarka. Laifinmu nā da yawa, amma tēkun jin-ƙanka, bā ya da iyāka. Ka tsayar da mu, kuma ka ƙarfafā mu.Taimakar mu, dōmin mu karɓu gaban fādarka. Haskaka zūkāce, maida idānu wāyeyyu, da kunnuwa māsu ji, warkar da marar lāfiya, kuma rāya matattu. Arzuta matalauta, kuma ka amintar da māsu faƙēwa. Karɓar mu cikin īkonka. Haskē mu da hasken alhēri.
Kai nē mai karāma! Kai nē mai jin-ƙai! Kai nē mai taimakon tālikai.
Yā Allah, ka būɗa ƙōfa, ka bāda hāli, ka sā hanya ta zama shiryayya, ka tsāga daji, don mu sāmu jagōra har zuwa wajen waɗannan rāyukan da ka shirya zukacensu zuwa ga addininka, kuma dā dai ka tūro su wajenmu. Kai nē rāhimi mayalwaci, mabuwāyi.
Sūnanka ya girmama yā Allāna. Yanzu da ka sā ni hanyar gāne gaskiya, ina rōƙon ka, daga sūnanka wanda ya fi ƙarfin a kwatamtā shi da harshe kō da rubūtu, sūnanka wanda ka ɓōye har abadin ābāda, kuma wanda zā a rika ɗaukakāwa har kullum, ina rōƙon ka sā, nan da ƙārēwar shēkarar nan, tūtar īkonka ta ƙāra hayēwa, dūniyar nan ta wadāta da arzikinka, ta dukufa cikin fargā da hanyar saninka da kusanta da kai, kuma kōwa ya tāshi tsaye don ya bāda wa’azin addininka. Lalle, kai nē mabuwāyi, mai girma, karīmin, mai kōmi, kuma mai aikata abun da yake sō.
Yā Allah Ubangijina! Kō da yake nī bā kōwa nē ba, kuma bā ni da wata gwaninta, gā ni ɗauke da haramar aikata babban abu, sabōda nā ɗauki niyar baza kalmarka, kuma nā shirya wātsa addininka cikin dūniya gabāɗaya. Nā san sarai, bā ni da ƙarfin cika wannan aiki, in bā kai ka taimakē ni ba da rūhu mai tsarki. Ka bā ni nasara da taimakon malā’ikunka na samāniya, ka sauko mani īkonka, wanda yake maida ƙuda ya zama shirwa, ɗason ruwa ya zama tabki har mā ya zama tēku, ƙwāyar ƙasa ta zama tarmāmuwa mai haske.
Yā Ubangiji, ka shirya ni da īkonka mai nasara, kuma da ƙarfinka mai rātsa kōmi da kōwa, don harshēna ya iya yaba ka, kuma ya maka kirāri cikin halittarka, don kuma zūciyāta ta cika da ƙaunarka, kuma da saninka.
A gaskiya, ka na da īkon yin abunda ka ga dāma, mulkinka yā mallaki kōmi da kōwa.
Ya kai Allah, mafi kwatamci, yā kai Ubangijin tālikai! Rāyukan nan sū ne jāruman nan nāka na samāniya. Ka dāfa musu, yanda da taimakon malla’ikun samāniyarka, zā su ci nasara. Ka sā kōwane rai, ya ciyō kan wannan karkara, da ƙaunar Allah, kuma da hasken wa’azin Ubangiji. Yā Allah ! Ka zama kai nē madōgari da mataimaki a garēsu cikin hamāda, tudunnai kō fadama, ƙunci kō shāya, kō tēku, ka amince da su, don su sā a ji kiranka a cikin hikimarka da īkonka.
A gaskiya, kai nē mabuwāyi, mai ƙudura, masanin kōmi, ƙadīran. Kai nē mai basīra, mai ji, mai gani.
Dukan yabo yā tabbata a garēka, yā Allah Ubangijina ; kai da kake tūshen girma da ɗaukaka, sarauta da mulki, natsuwa da alhēri, mai ban tsōro da īko. Ga wanda ka ga dāma, ka kan jāwo shi, kusa da mahīhīcin tēkunka mai girma. A kan wanda ka nufa, ka kan sanarshē shi da sūnanka na fil azal. Ga duka waɗanda kē sama da ƙasa, bā wanda zai iya tsayāwa ga nufinka mai girma. Tun fil azal, kā yi mulkin halittarka, kuma zā ka ci gaba da mallaƙar abin da ka hālittō da īkonka. Bā wani Ubangiji sai kai, mafi girma, mafi ɗaukaka, mafi īko da basīra.
Ka haskaka huskōkin bāyinka, dōmin su gan ka, ka wanke zukātansu, dōmin su jūya zuwa sāmun ni’imarka, kuma su bāda gaskiya ga wanda ya bayyana asīranka da babbar alfurmarka.
Bā shakka, kai nē Ubangijin duka dūniya. Bā wani Allah sai kai, mai nasara, mai mallaƙar kōmi.
Yā Allāna, abun ƙaunāta, majibincīna, abun bukātāta! Da wane irin halshē zan iya bayyana iyākacin gōdiyāta zuwa garēka ? Ina cikin duhu, kā wāyar da ni. Nā huta daga hanyarka, kā maidō ni cikin alfurmarka. Nā zamana kamar matacce, kā rāyar da ni da ruwanka mai rāyarwa. Nā ƙēƙashe, ka falfaɗō ni da ruwan samāniyar kalmarka da suka zubo daga alkalamin rāhimi.
Yā kai ƙaddara ! Bābu sāmun wata rāyuwa in bā ƙalƙashin alhērinka bā. Kar ka kauce mana da kyautatāwarka, kuma kar ka kai mu nēsa da kōgin rahamarka. Ina rōƙon ka taimakē ni, a kullum, kuma a kō’ina, ina rōƙon ka, daga samāniyar alfurmarka, ka sauko mani da wannan alfurma tāka ta tun fil azal.
A gaskiya, kai nē Ubangiji mayalwaci, mai mallaƙar kōmi da kōwa.
Ka cē : ɗaukaka ta tabbata a garēka, kai da ka sā duka waliyyai suka yarda da kāsāwarsu gaban cikakken īkonka, kuma ka sā kōwane manzonka, ya tabbata cēwa, shi bā kōmi nē ba gaban managartacciyar ɗaukakarka marar iyāka.
Ina rōƙon ka, don girman sūnanka, wanda ya būɗe ƙōfōfin samāniya, kuma ya cika rūhunan dake samāniya da ƙaunarka, ka sā ni in dāce don in bautā maka, kuma ka bā ni ƙarfin da zai sā ni in shiryu, in bi umurnin kitābinka.
Kā san abun da yake tāre da ni, yā Ubangijina, amma nī, ban san abun dake tāre da kai ba. Kai nē ƙadīran masani.
Martaba ta tabbata ga sūnanka, yā Ubangiji Allāna! Kai nē wanda kōmi da kōwa yake bautāma, amma bā ka bautāwa kōwa, kai nē mamallakin kōwa da kōmi, amma bābu mai mallakarka. Kai nē masanin kōmi da kōwa, amma kā fi ƙarfin a san kōmi nāka.
Da ka sō mutane su san ka, sai da kalmarka guka ɗaya, ka rāya dūniya, kuma ka halicci duk abun dake sama da ƙasa. Bābu wani Allah sai kai, mahalicci, mai rāyāwa, maɗaukaki mabuwāyi.
Ina rōƙon ka, da wannan kalma da kā sauko daga irādarka, ka bā ni izinin shan ruwan nan rāyayyu, da ka rāya zukācen zāɓɓaɓun bāyinka, ka wanke rūhun māsu ƙaunar ka, in sāmu īkon mayar da fuskāta wajenka, kullum, kuma cikin kōwane hāli.
Kai nē Jalla sarkin sarauta, mayalwaci. Bābu wani Allah illā kai, mai shirya kōmi, maɗaukaki masani.
Yā Allah, ka haske wannan ƴar halittar tāka, ka ƙarfafa ta, ka ilimintar da ita, kuma kōwace sāfiya, ka ƙārā mata kuzāri ta zamanto tana ƙalƙashin kāriyarka, don ta tsīra ga duk wani zunubi, dōmin ta zama mai bauta maka, mai maido ɓatattu bisa hanya, mai jāgōrancin marassa ƙarfi da marassa dūkiya, mai ɗiyautar waɗanda sun zamana bāyu nē, kō suna cikin wahala, ta zama mai jin dāɗi ta hanyar tunāninka. Kai nē ƙadīran, mai basīra.
Yā Allah, ka tarbiyartar da yāran nan. Sūne itātuwan lambunka, sūne furannin fadamarka, kuma sūne wardin garkarka. Dā dai ruwan samāniyarka, ya zubo musu, rānā mai rāyarwa, ta haskēsu da ƙaunarka. Dā dai sanyin bazarka, ya sanyayā su, dōmin su sāmu kyaukyāwan jāgōra, su girma bā tāre da karkatā ba, kuma su zamana tamkar madūban kyāwonka mai tsarki. Kai nē mayalwaci, mai jinƙai
Yā Allah, ka sā ni hanya, ka kāre ni, ka haskaka futular zūciyāta, kuma ka maida ni tamkar tarmāmuwa mai haske. Kai nē mai īko, mabuwayi.
Yā Allah ! ka rāyar da wannan jinjiri cikin hannun ƙaunarka, kuma ka bā shi nōnon ƙaddararka. Ka shibka wannan matāshiyar itāciya cikin lambun ƙaunarka, kuma ka bā ta ruwan gizāgizan alhurmarka. Ka sā ya zama yāron daularka, kuma ka tafiyar da shi wajen dūniyar samāniyarka. Kai nē mai cikakken īko, mai jinƙai! Kai nē mai bādāwa, mai yalwatāwa, wanda alhērinka ya hiye kōmi.
Yā kai Allah wahābu, nī ƙaramin yāro nē, ka girmar da ni, kuma ka karɓē ni cikin daularka. Nī mazamnin dōron ƙasa nē, ka maida ni mazamnin samāniya. Nī mutunen wannan dūniyar nē, ka būɗē mani ƙōfar daular samāniya. Ina cikin baƙin rai, ka yardē mani, in sāmu farin ciki; Nā rungumi abun dūniya, ka zunduma ni cikin tauhīdi, kuma ka yarde mani bayyana alfarma maras ƙārēwa. Kai nē mabuwāyi, mai cikkakar ƙauna.
Yā Ubangiji Allanā! nī yāro nē ƙarami. Ka cīda ni da nōnon rahamarka. Ka rāyar da ni cikin ƙaunarka, ka karantar da ni a makarantar nasīyarka, kuma ka sā, in girma cikin inuwar karāmarka. Ka zāro ni daga cikin duhu, ka maishē ni tamkar fitila mai haske. Ka ƙēɓē mani masīfa, ka sā, in tōfō cikin lambun furanninka. Ka sā ni cikin māsu bautā mā a fādarka, kuma ka bā ni hālin ādalai. Ka sā, in zama dalīlin albarkar bil’adama, kuma ka ɗaura mani rawanin rāyuwa ta har abāda. A gaskiya, kai nē mai ƙarfi, mai ƙudura, mai gani da kuma ji.
Wannan salla ta zanā’ida, ana yin ta zuwa ga mariganyi baha’i mai shēkaru gōma sha biyar (15) a ƙalla. Wannan salla ita ƙadai cē ake iya yi a jam’i. Baha’i guda yake karantā ta gaban sauran mutāne da suke sahu a tsaye. Bā dōle ba nē, su jūya sahunsu wajen ƙibla.
Yā Allāna, gā bāwanka , ɗan bāwanka, da ya bāda gaskiya a garēka, kuma ya yarda da alāmōminka, yā jūya fuskarshi wajenka, bai sarƙafa da kōmi ba, in bā kai ba.
A gaskiya, kai nē mafi rahama cikin māsu rahama. Ka karɓē shi cikin samāniyar alhērinka da tēkun alfurmarka, yā kai mai gafartāwa ƴan adam, kuma mai ɓōye laifunsu! Ka yi masa marhaba cikin dandalin rahamarka mafi kwatamci, da kē nan kāfin halittar sama da ƙasa.
Mai karanta wannan salla, ya jā ‘’Allah’u’Abha’’ sau shidda (6), kuma ya jā kōwace āyā mai zuwa, sau gōma shā tara (19).
Allah’u’Abha (sau1)
A gaskiya, mū duka muna ƙaunar Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna durƙusāwa gaban Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna rōƙon Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna yabon Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna gōdiya ga Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna bin umarnin Allah (sau 19)
A cikin Kitābil Akdas, Ubangiji yā cē : ‘’Mun umurci mutun da yin azumi da zāran yā kai shēkara gōma shā biyar. Wannan umurnin Allah nē, Ubangijinku da Ubangijin uwāyenku. Māsu balāguro, marassa lāfiya, da māta masu jūnā biyu, kō māsu bāda nōnō, ba a umurce su da yin azumi ba. Idan kuna azumi, kada ku shā ruwa, ko ku ci abinci daga fitōwar rānā, zuwa fāɗuwarta, kuma kada ku yarda nishāɗi ya hana ku sāmun wannan ni’ima da aka rubūta a cikin littāfi. Ana azumi daga cikin watan Ālā.
Yā Allāna, don darajar āyarka mai ƙarfi, kuma da wahayin zuwa ga ƴan adam, ina rōƙon kada ka rufe mani ƙōfar birnin kasancewarka, kuma kada ka kunyata gūrīna da na sarƙafa ga bayyanar falalarka tsakānin halittunka.
Kana gani nā, yā Allāna, ina sarƙafe ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar muryarka mai zāƙi, kuma da maganarka mai girma, ina rōƙon ka jāwo ni kusa da dakalin ƙōfarka, kuma kada ka riƙe ni nēsa da inuwar rahamarka, kō zauren yalwarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, gaban kyaukyawar huskarka, kuma da kansancēwarka dake wātsa haske daga jiririn samāniyar ƙōli, ina rōƙon ka jāwo ni, in ji ƙamshin turāren tufāfinka, kuma ka bā ni dāmar jin maganarka mai zāƙi.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, dōmin gāshinka dake shāre fuskarka, da al’ƙalaminka maɗaukaki da yake rubūtu bisa shāfin āyōyinka, yana baza ƙamshin turāren muskin ɓōyayyun fusā’ō’i. Ina rōƙon ka taimakē ni, in kyautatāwa addininka, bā tāre da kāsāwa ba, kuma habaicin waɗanda suke adāwa da āyōyinka, kō suka juyāwa fuskarka bāya, su kāsa dabaibaye ni.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar sūnanka da ka naɗā shīnē, sarkin sūnāye, da yake ƙarfafa duk waɗanda ke sama da ƙasa, ina rōƙon ka bā ni ƙarfin tsinkāyar rānār kyāwonka, kuma ka zubo mani zaƙamin maganarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar tantin martabarka dake kafe a ƙōlōluwa mafi tsayo, kuma da zauren wahayinka dake bisa tudunnai mafi tsayi, ina rōƙon ka taimake ni da yalwarka don in aikata abunda nufinka yake buƙāta, da abunda shariɗōɗinka suka bayyana.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar kyāwonka mai haske a sararin dūniya na har abada, kyāwo wanda daga ɓullōwarsa daular kyāwo da kanta take masa sūjada, kuma take ɗaukakāwa da babbar murya. Ina rōƙon ka taimake ni, in rabu da duk abūbūwan da garēni, kuma in rāyu da abunda yake nāka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar bayyanar sūnanka, wanda shīnē abun ƙauna, wanda ya sā zukātun mumminai suka ƙōne da wutar sōyyaya, kuma ya sā rāyukan mazaunan dūniya suka haye wajensa. Ina rōƙon ka tallafē ni, in tuna da kai cikin halittunka, kuma in yabā ka cikin al’ummarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hannyar ƴāƴar iccen ɗaukakarka, da būsāwar bazarar sanyin bayyanarka cikin daular sūnāyenka, ina rōƙon ka nīsanta ni da abunda kake ƙyāma, kuma ka jāwo ni kusa da wurin da sahiyar alāmunka ta ɓullo.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar wannan baƙi, wanda daga fitōwarsa daga bākin irādarka, ya sā tēkuna suka kumbura, iska ta būso, ƴaƴan itāce suka fito, itātuwa suka tsiro, ya shāfe tsōfōfin ajjiya, ya kēce duk wani lulluɓi, kuma ya gaugauta mumunai wajen hasken fuskar Ubangijinsu mai ƴanci. Ina rōƙon ka sanarshe ni da abun dake ɓōye cikin zurfin arzikin iliminka da asūssun hikimarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar wutar sōyyayarka da take kōre kwāna daga idānuwan zāɓɓaɓun bāyunka da masōyanka, kuma dōmin ambatarka da suke tun assuba. Ina rōƙon ka sā ni cikin sahun waɗanda suka kai ga abun da ka bayyana cikin kitābinka, kuma ka ƙayyada cikin irādarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafe ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar hasken kasancēwarka da take sā māsu ƙaunarka su gabāci kibiyōyin ƙudurarka, kuma ta sā mabiyanka su fuskanci takubban maƙiyanka, cikin hanyarka. Ina rōƙon ka bayyana mani, abun da alƙalaminka mai tsarki ya bayyanāwa aminnanka da zāɓāɓɓun bāyunka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar sūnanka dake saurāren kiran masōyanka, da ajjiyar zūcin waɗanda kē ƙaunar ka, da kūkan waɗanda suke kusa da kai, da nīshin mabiyanka, ta hanyar sūnanka da yake cinma gūrin waɗanda suka danganta da kai, suke kai ga jin dāɗinsu ta wajen alfurmarka da yalwarka, ta hanyar sūnanka dake sā tēkun gāfartāwa ya zāburo gaban fuskarka, kuma kyautarka ta zubo bisa māsu bautā maka. Zuwa ga duk waɗanda suka jūya wajenka, suna yin azumin da ka umurcē su da yi, ka rubūta lāda ga wanɗanda bā su magana sai da izininka, kuma suka yi wātsi da duka abūbūwan da garēsu, dōmin ƙaunarka bisa hanyarka.
Ta hanyarka da alāmu da hujjōjinka, ta hanyar hasken rānar kyāwonka da rassunka, ina rōkon ka shāfe laifin waɗanda suke bin dōkōkinka, suna yin abūbūwan da ka umurcē su da yi cikin kitābinka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yabo ya tabbata a garēka yā Ubangiji Allāna. Ina rōƙon ka, don darajar wannan bayyana, da ta maida duhu haske, kuma da garēta a ka gina masallacin jama’a, da garēta kuma aka sauko rubutaccen allo, a ka shinfida ɓoyayyan kundi, ina rōƙon ka sauko mana, ni da abōkan zamāna, abun da zai sā mu hira wajen samāniyar ɗaukakarka, kuma abun da zai tsarkakar da mu da dauɗar shakka da ta hana waɗanda ba su amince ba, shiga cikin zauren ɗayantakarka. Yā Ubangijina, gā ni, nī nē wanda ya sarƙafu ga igiyar alfurmarka, kuma ya rātayu ga zanen rahama da alhērinka. Ka zubo mana ni da duk waɗanda nike ƙauna, albarkan nan da ka wārewa zāɓaɓɓun bāyunka.
Yā Ubangijina, ga rānaikun da ka umurci bāyunka da ɗaukan azumi. Albarka ta tabatta ga wanda ya ɗauki ƙishurwa, kawai sabōda ƙaunarka, kuma cikin wātsi da kōmi in ba kai ba. Ka taimakē ni kuma ka tamaike su, yā Ubangijina, don mu bi umurninka, kuma mu tsaida dōkōkinka.
A gaskiya ka nā da īkon yin abin da ka ga dāma. Bābu wani Allah illā kai, mafi sani da basīra. Dukan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin duka dūniya.
Shīnē Sarki, Masani, Mai hikima ! Ka saurāri sūdar aljanna dake bisa rassun itāciyar dawwama har abada. Tana rēra tsarkakakkiyar wāƙa mai dāɗi, tana ayyanāwa rāyuka na gari, bushārar kusantaka da Allah. Tana gayyatar waɗanda suka bāda gaskiya da kaɗaitakar Allah, su isō dandalin mayalwaci. Tana gayāwa waɗanda ba su sarƙafu da abun dūniya ba, sāƙon da ya sauko daga Allah sarki, maɗaukaki, da bā shi abōkin tārayya. Tana jāgōrar mumunai zuwa wajen gadon tsarkaka, kuma wajen wannan nagartacen kyāwo.
A gaskiya, gā kyāwo mafīfīci, wanda aka ambata cikin littatafan manzonni, wanda ya zō dōmin ya bambanta gaskiya da ƙarya, kuma ya auna hikimar duka umurni. Gā itāciyar rāyuwa mai ɗauke da ƴāƴan ɗaukakar Ubangiji Allah, maɗaukakin sarki, mai ƙudura, mai girma.
Yā kai Ahmad ! Ka shaida da cēwa, a gaskiya, shīnē Allah, kuma bābu wani Allah illa shi, sarki, mai kārēwa, mafi kwatamci, mai kōwa mai kōmi, kuma wanda Ya aīko, da sūnan Ali, ma’aikin Allah nē, wanda ya cancanta mu karɓi umarninsa gabāɗayanmu.
Ka faɗī cēwa : yā ku al’umma, ku bi umarnin da Ya bā ku cikin Bāyan, Shī wanda shīnē maɗaukaki, mai hikima. A gaskiya, shīnē sarkin manzonni, kuma littāfinsa, shīnē Umul kitābi, idan dā kuna cikin māsu iya gānēwa.
Haka dai, tun daga cikin wannan kurkukun, sūdā take rēra kira a garēku. Shīnē ya cancanta da ya mīƙā muku wannan sāƙō. Wanda ya ga dāmā, ya yi wātsi da wannan galgaɗi, kuma wanda yake sō, ya zāɓi hanyar Ubangijinsa !
Yā kū al’umma, idan kun yi wātsi da waɗannan āyōyi, tō a kan wace hujja kuka dōgara imāninku ga Ubangiji Allah subahānahu wa ta āla ? Ku fiddō ta, yā ku tāron munāfikai ! Nā rantse da wanda kē riƙe da raina cikin hannunsa, bā zā su iyā ba yau, bā zā su iyā ba gōbe, kō dā sun haɗu suna tallafar jūna, dōmin yin haka.
Yā kai Ahmad ! Kada ka manta da alhurmāta idan nā ƙaura. Ka tuna da rāyuwāta cikin rāyuwarka, da matsalōlīna, kuma da kōrar da aka mani zuwa wannan manīsancin kurkuku. Ka tsaya tsayin daka cikin ƙaunāta, kada zūciyarka ta firgita, kō dā takubban maƙiyanka zā su sassāre ka, kō kuma sama da ƙasa su kai maka hari.
Gaban maƙiyāna, ka zamana tamkar wutar garwashi, gaban masōyāna, ka zamana kōgin rāyuwar har abada, kuma kada ka shiga cikin māsu shakka. Idan bisa hanyāta, matsala tā sāme ka, kō sabōda ƙaunāta, an cī maka mutunci, kada ka dāmu.
Ka dōgara ga Allah, Ubangijinka, Ubangijin ubanninka, alhāli mutāne suna ɓata bisa hanyōyin zato, bā su iya ganin Ubangiji da idānuwansu, kō su ji muryarsa da kunnuwansu. Haka dai muka tardō su, kamar yadda kake gani. Camfinsu, yā zame musu yānā, tsakaninsu da zūciyarsu, yana rufe musu hanyar Ubangiji Allah maɗaukakin sarki.
Ka tabbata cikin zurfin zūciyarka da cēwa, wanda ya yi wātsi da wannan kyāwo, yā yi wātsi da manzonnin dauri, kuma har abadin ābāda, yā gwada fāɗin rai ga Allah Ubangiji subahānahu wata ālā.
Kafa wannan āyā cikin zūciyarka, yā kai Ahmad ! kuma ka jā ta har mutuwarka, kada ka kēɓē daga bisa hanyar umurninta. Haƙīƙa, wanda ya jā wannan āyā, Allah yā ɗauki alkawarin bā shi lādan shāhidai ɗari, kuma da izinin kyautatāwa dūniya da lāhira. Wannan alhurmā, mun bā ka ita cikin rahamarmu da karāmarmu, dōmin ka zamana cikin māsu gōdiya.
Nā rantse da Allah Ubangiji subahānahu wata ālā ! Duk tālikin dake cikin matsala, kō rūdāni, idan ya jā wannan āyā da zūciya guda, Allah nā sanyayā masa zūciyarsa, ya ƙēɓē masa azabar da yake ciki, kuma ya rabā shi da matsalōlin da suka addabē shi.
A gaskiya, shīnē mai rahama, mai jin ƙai. Gōdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin duka dūniyōyi.
Da sūnan Allah, madawwami, mafi girma. A gaskiya, zūkācen aminnai nā tōyēwa cikin wutar rabuwa: Inā ƙyalƙyalin hasken fuskarka, yā kai abun ƙaunar dūniyōyi?
Waɗanda suke kusanka, gā su cikin duhun rūdāni: Inā ƙyalƙyalin sāfiyar haɗuwa da kai, yā kai abun bēgen dūniyōyi?
Jikin zāɓāɓɓunka suna konce suna shēƙa bisa turɓuwa mai nīsa: Inā tēkun kasancēwarka, yā kai mai wadātar da dūniyōyi?
Gā hannuwa māsu rōƙo nā nufa wajen samāniyar alfarmarka da karāmarka: Inā ruwan alhērinka, yā kai da kake ƙāyatar da dūniyōyi?
Azzāluman kāfirai nā ɓullōwa daga kō’ina: Inā īkon alƙalamin dōkōkinka da bā a gōcēwa, yā kai mai nasara bisa dūniyōyi?
Ana jin karnuka nā habshi daga kō’ina: Inā zākin dājin ƙarfinka, yā kai mai hukunta dūniyōyi?
Ɗāri na suƙe ƴan adam gabāɗayansu: Inā gumin ƙaunarka, yā kai mai zāzafa duniyōyi?
Balā’i yā kai matuƙa: Inā alāmōmin tallafinka, yā kai mai cēton dūniyōyi?
Baƙin duhu yā lulluɓe yawancin al’ummmōmi: Inā hasken martabarka, yā kai mai ƙāwata dūniyōyi?
Ƙēyōyin mutāne sun yi gautsi dōmin ƙēta: Inā takubban fansarka, yā kai mai ragwargwaza dūniyōyi?
Sākarci yā kai matuƙa: Inā tūtōtin ɗaukakarka, yā kai maɗaukakin dūniyōyi?
Darūra tā māmāye wanda ya bayyana sūnanka: Inā murnar assubāhin bayyanarka, yā kai dāɗin dūniyōyi?
Rūɗāni yā māmāye duka al’ummōmin dōron ƙasa: Inā tūtōtin fara’arka, yā kai murnar dūniyōyi?
Kana ganin ana lulluɓe gabashin alāmōminka da habaicin sākarci: Inā yātsun īkonka, yā kai mamalakin dūniyōyi?
Ƙishirwa mai tsanani tana kāda duka ƴan adam: Inā gulbin karāmarka, yā kai arrahamānin dūniyōyi?
Haɗama tā mallaki duka ƴan adam: Inā wanda sū nē shaidar dangana, yā kai Ubangijin dūniyōyi?
Kana ganin wannan, wanda aka zālunta shī kaɗai cikin hijirarsa: Inā rundunōnin samāniyar hukuncinka, yā kai sarkin dūniyā?
An bar ni cikin ƙasa da bā tāwa ba: Inā tūtōcin amānarka, yā kai madōgarin dūniyōyi?
Mutuwa nā gabātar duka ƴan adam: Inā ambāliyar tēkun rāyuwarka, yā kai rāyuwar dūniyōyi?
Raɗe-raden nalīsa nā rātsa yawancin mutāne: Inā garwashin wutarka, yā kai fitilar dūniyōyi?
Dāɗin annashuwa nā rāzana yawancin mutāne: Inā tāhirin jijjibi, yā kai abun bēgen dūniyōyi?
Kana ganin zālunci yana murƙushe wannan bāwan Allah a ƙasar sīriya: Inā ƙyalƙyalin haskenka da ya fāra kunnōwa, yā kai hasken dūniyōyi?
Kana ganī an hanā ni magana: Daga inā āyōyinka zā su ɓullo, yā kai sūdar dūniyōyi?
Shirmē da tunānin wōfi sun dabaibaye yawancin mutāne: Inā māsu fasara gaskiyarka, yā kai hakīkar dūniyōyi?
Bahā nā lumēwa cikin tēkun azāba: Inā al’arshin tsīrarka, yā kai mai kubtar da dūniyōyi?
Kana ganin sāfiyar kalmarka tā ɓace cikin duhun halitta: Inā rānar samāniyar alfarmarka, yā kai jāgōran dūniyōyi?
Fitilōlin gaskiya da tāhir, biyyaya da ɗiyauci sun mutu: Inā alāmun fushinka mai rāmāwa, yā kai injin dūniyōyi?
Bābu kō mutun guda da ya kāmāwa Manzonka, kō ya yi nazari bisa matsalōlin da ya gabātar bisa hanyar ƙaunarka: Gā shi alƙalamīna ya būshe, yā kai masōyin dūniyōyi?
Iskar ƙaddara ta karya rassun iccen aljanna, sun zuɓe a ƙasa: Inā tūtōtin āgajinka, yā kai mai kāre dūniyōyi?
Ƙūrar ba’a tā ɓōye wannan fuskā: Inā bazarar jinƙanka, yā kai arrahamānun dūniyōyi?
Al’ummar munāfikai nā ɓāta rigar tsabta: Inā taguwar tsarkakarka, yā kai mai suturar da dūniyōyi?
Ayyukan mutāne nā dākatar da tēkun alfarma: Inā igiyōyin karāmarka, yā kai abun bēgen dūniyōyi?
Zāluncin maƙiyanka, sun kulle ƙōfar dake kai garēka: Inā mabūɗin alhērinka, yā kai mai būda ƙōfōfin dūniyōyi?
Iskā mai ɗauke da gubar adāwa nā ƙēkāshe ganyāye: Inā yayyafin gizāgizan karāmarka, yā kai mayalwacin dūniyōyi?
Ƙūrar zunubi, nā duhuntar da sararin samāniya: Inā bazarar gāfararka, yā kai mai gāfartāwa dūniyōyi?
Wannan matāshi, yana nan shī kaɗai cikin hamāda: Inā rūwan alfarmarka ta samāniya, yā kai mai baiwā dūniyōyi?
Yā alƙalamin ƙōli, mun ji kiranka mai dāɗi cikin daula madawwamiya: ka shūrāri abun da harshen girmā yake faɗi, yā kai ma shā wuyan dūnoyōyi?
Idan bābu ɗāri, yāyā gumin kalmarka zai bayyana, yā kai mai fasarar da dūniyōyi?
Idan bābu balā’i, yāyā hasken rānar jūriyarka zai ganu, yā kai hasken dūniyōyi?
Kada ka yi jājē sabōda maƙētatā. An halittō ka don a ƙuntatā maka, kuma ka yi jūriya, yā kai mahaƙurcin dūniyōyi?
Bayyanarka cikin māsu adāwa a jiririn alƙawalinka, abun nishāɗi nē, kuma jūyāwa wajen Allah abun jin dāɗī nē, yā kai ƙaunar dūniyōyi!
Kā kafa tūtar ƴanci bisa ƙōlōluwar birji, kuma kā ɓullo tēkun karāma, yā zumūɗin dūniyōyi!
Kaɗaitakarka nā gwada ƙyalƙyalin rānar ɗayantaka, kuma hijirarka nā ƙāyatar da ƙasar kaiɗaita. Ka yi jūriya, yā kai bāƙon hauren dūniyōyi!
Mun maida ƙasƙantā tamkar rigar ɗaukakarka, azāba adon gidan ibādarka, yā kai abun kirārin dūniyōyi!
Kana ganin zukāce cike da ƙiyayya, tō ka yi haƙuri, yā kai da kake ɓōyē zunubban dūniyōyi!
Idan an zāro maka takōbi, kada ka jā da bāya: idan an halbō maka kibiya, ka gaggauto ka nufē ta, yā kai sadaukin dūniyōyi!
Kai zā ka zubda hawāye, kō nī zan zubda? Yā cancanta in yi kūka gaban māsu kārē ka dake ƙalīlan, yā kai tūshen kōke-kōken dūniyōyi!
Hakīka, ina jin kiranka, yā kai mafi ɗaukaka, abun ƙauna! Yanzu zāfin azāba da wutar kalmarka mai armashi nā haskaka fuskar Bahā. Sai ya gabāci wurin sadaukarwa cikin amāna, yana son kaiwa ga abun da kake sō, yā kai mai shirya dūniyōyi!
Ya kai Ali Akbar, ka gōdēwa Ubangijinka dōmin wannan allo. Kana iya jin ƙamshin tawālina, kuma ka gāne da rūdānin da muka gabāta bisa hanyar Ubangiji Allah subahānahu wa ta āla, wanda kōwa yake wā ibāda. Bāwan da ya jā, kuma ya yi nazari bisa wannan āyā, wuta nā kunnuwā cikin jījīyar jininsa, da zā ta māmāye dūniyōyi.
Da sūnan wanda aka haifa a wannan rāna, wanda Allah ya haliccē shi dōmin ya zama kākākin sūnansa mai īko, mai ƙauna.
Gā allon da muka bayyana a wannan dare da sama da ƙasa suka haskaka da hasken da ya baza ƙyalƙyalinsa bisa duk halitta.
Yā kai wannan dare ! yabo ya tabbata a garēka, sabōda daga garēka nē rānar Ubangiji Allah ta fito, rānar da cikin ƙudirinmu, zā ta zamana fitilar tsīra ga duka mazaunan birānen sūnāye, kuma da ita cē kambun nasarar zakarun dake cikin fagen fāmā na har abada, kuma da ita cē assubāhin murna da zumūɗi ga duk halitta.
Yabo matuƙa ya tabbata ga Allah Ubangiji, mahaliccin sammai, wanda ta garēshi wannan rānā ta ambaci wannan sūna, ta kēcē lābilan zatuttuka na wōfi, ta shūɗē yanannakin tunānin banza, kuma da garēta sūnansa na innanaha, ya bayyana a jiririn hakīka. Ta garēka nē aka būɗē tūlun ruwan rāyuwa har abada, aka būɗē makullin ƙōfōfin sani da na kalma ga idānuwan al’ummōmin dūniya, kuma bazarar Arrahamānu ta būsa a kōwane wajāje. Ɗaukaka ta tabbata ga wannan sā’i da cikinsa nē alfarmar Ubangiji, mai īko, masani, mai hikima ta bayyana !
Yā kē majalasar sama da ƙasa ! Wannan nē daren farkon da Allah ya sō shi da zama alāmar dare na biyu da aka haifi Wanda bābu kirārin da ya isa ya kwatanta matsayinsa. Murna ta tabbata ga wanda ya yi tunāni bisa waɗannan darāre biyu : a gaskiya zai gāne da cēwa, kasancēwarsu da ake gani tā daidaita da tūshensu na ainafi, kuma zai gāne ya fahimta da gaibunan da suke ƙunshe a cikin wannan wahayi, wahayin da ta garēshi nē ginshikan īmānin ƙarya suka rūshe, gumāken camfi suka tarwatse, kuma aka warware tūtar dake furucin cēwa « Bābu wani Allah illā Shī, mai īko, al malīku, mafi kwatanci, mai kārēwa, Al azīzu, da ya fi a kai garēshi ».
A wannan dare nē, ƙamshin turāren kusanta ya bazu, ƙōfōfin haɗuwa a rānēkun ƙarshe suka būɗe warai, kuma duk halitta ta gilgizu tana faɗa cēwa : « Daula ta Allah cē, Ubangijin duka sūnāye, shī da ya zō da mulki na musamman ya mallaki dūniya gabāɗayanta !». Wannan dare, majalasar samāniya tā karrama yabon Ubangijinta, Al’malīku, Maɗaukakin Sarki, kuma gaskiyar sunāyen Allah ta yi yabon Wanda Shīnē sarkin farkō da ƙarshe a wannan wahayi, wanda ƙarfinsa ya sā tsaunika suka zāburo zuwa wajen wanda ya isa ga kōmi da kōwa, mafi ɗaukaka, ya jūya zukācen masōya wajen fuskar masōyinsu, ya sā bazarar ƙauna ta mōtsa ganyāye, cikin murna, muryōyin itāce suka amshi kiran wanda bā shi da iyāka. Duka dūniya ta yi gilgiza cikin bēgen kaiwa ga Sarki madawwami, kuma wannan kalmā ɓōyayyā ta bayyana cikin īkon sūnā, ta maida kōmi ya zama sābo.
Yā kai daren Al’karīmu ! A gaskiya, a garēka muna ganin umul kitābi. Shin, kitābi nē, kō kuma haifaffan ɗā nē ? Āā, nī da kaina nā shaida cēwa ! waɗannan batūtuwa na daular sūnāye nē alhāli kuwa, Allah Ubangiji yā ɗaukaka wannan kitābi sama da duka sūnāye. Ta wannan kitābī nē, gaibu ɓōyeyye da ingantaccen sirri suka bayyana. Nā rantsē da rāyuwāta cēwa, duk abun da aka ambata na daular laƙani nē, alhāli umul kitābi nā sama da duk waɗannan abūbūwa. A garēshi nē alāmun « Bābu wani Allah sai Allah » suka bayyana sama ga kōmi. Nā shaida cēwa, kō da yake kōwa yā san da haka, kamar yanda Ubangijinka ya sanar, kunnansa nē kawai yake iya jin su. Murna ta tabbata ga wanɗanda suka amince da wannan !
Sai cikin māmāki, alƙalamin Mai sama ya yi kira cēwa : « Yā kai wanda kai nē ɗaukakakke sama ga duka sūnāye ! īnā rōƙon ka, don girman īkonka da ya mallaki sama da ƙasa, ka sauke mani nauyin ambatar ka, sabōda nī kaina, nā kasance don īkonka mai rāyāwa. Ta ƙāƙā zan iya kwatanta duka abūbuwan da duk halitta ta kāsa kwatantāwa ? Amā fa, nā rantse da ɗaukakarka, idan na furta ilhāmar da ka sā a raina, duk halitta gabāɗayanta, zā ta mutu don murna da jin dāɗi, abun dake nūna cēwa, a wannan haskekken wuri maɗaukaki wanda ya wuce kōmi, wannan halitta zā ta gamsu gaban tēkun kalmarka. Yā Ubangiji, ka yardēwa wannan alƙalami mai wata-wata, ya dēna kirārin wannan muhimmin matsayi, kuma ka dūbē ni da idon rahama, yā kai Sarkīna Ubangijina. Ka manta da kuskurēna a gabanka. A gaskiya kai nē Ubangijin falalā, Mai īkō, mai gāfartāwa kullun, Al’karīmu.
(Ayyan-i-Tis’ih shāfi 12 zuwa 15)
Shīnē tsarkakakke, maɗaukaki, Mafi girma
Rānar bukin karramāwa cē, wandan shīnē kyāwon Ubangiji Allah, jabbāru, mai īko, mai ƙauna, yā hau gadon īkonsa. Murnā ta tabbata ga wanda, a wannan rānā ya kai garēshi, kuma wanda Allah, mai cēto cikin matsala, madawwami, ya dūbi wajensa. Ka cē: Mun karrama wannan buki cikin kurkuku mafi girma, a lōkacin da sarākunan dūniya suka tāshi suka yāƙē mu. Ammā fa, ƙarfin azzālumai har abada bā ya iya jā da mu, kuma rundunōnin dūniya har abada bā su iya murƙushe mu. Haka Arrahamānu yake shaidāwa.
Ka cē: ashē yā cancanta a tūre tūshen hakīkantaka gaban sūrūtan al’ummōmin dūniya? Ā’ā, nā rantse da kyāwonsa dake haske duk abūbuwan dā da na gōbe! A gaskiya wannan cē alfarmar Ubangiji da take lulluɓē duk halitta, kuma haka nē īkonsa da ya mallaki duk abūbuwan dake gani da duk abūbuwan da ake gani. Ku riƙe igiyar muhimmin īkonsa, kuma ku ambaci Ubangijinku mai ƴanci, a wannan assubāhi da haske yake gwada duk gaibu ɓōyeyye. Haka nē madawwami ya faɗa a wannan rānā da aka būɗe zāɓeɓɓen ruwa. Ku yi hattara, kada tunānin shirmen waɗanda suka ƙi yarda da Allah su tāda hankulanku, kō kuma zatuttukansu na wōfi, su nīsantā ku da madaidaiciyar hanya.
Yā kē al’ummar Baha! bisa fukāfukan dangana, ki hira ki shiga cikin sararin ƙaunar Ubangijinki, mai rahama, kuma ki tāshi dōmin ki kai Ubangijinki ga nasara, kamar yanda ādanannun alluna suka ƙadarta. Kada ki yi jāyayya da kōwa cikin bāyūna. Ki mīƙā musu zāƙin tsarkakakkun kalmar Ubangiji, sabōda, da īkonta nē mutāne suke iya sāmun dāmar jūyāwa wajensa. Duk waɗanda a yau, ba su kula da Allah ba, sun ɓata cikin shāwarsu, cikin ba su mā gāne ba. Murna ta tabbata ga wanda, cikin ƙasƙanta da tawāli’u, ya jūya fuskarsa wajen assubāhin āyōyin Ubangijinsa.
Yā cancanta ka tāshi ka karantar da mutāne bisa abun da aka bayyana cikin kitābin Ubangijinsu, mai īkō, mai ƴanci.
Ka cē: ka ji tsōron Allah, kuma kada ka kula da zatūttukan wōfi da waɗanda suke tafiya bisa hanyar shakka da rishin ādalci suke faɗa. Da zuciya mai armashi, ka jūya wajen fādar Ubangijinka, mamallakin duka sūnāye. A gaskiya, zai taimakē ka da ƙarfin gaskiya. Bābu wani Allah illā Shī, mai īko, mai cikakkiyar kyauta.
Yana yiyuwa ka gaugauta zuwa ga ƙaramin tabki, alhāli gā babban tēku nan gaban idonka? Ka jūyā gabādayanka wajensa, kada ka bi sāwun kōwanne daga cikin kāfirai maƙaryata. Tsuntu madawwami nā wāƙā bisa rassun itāciyarmu ta Ubangiji. Nā rantse da Ubangiji Allah! wāƙarta guda ɗaya tak, tā isa ta shāwar da majalasar samāniya, har mā, mazaunan birānen sūnāye, kuma har mā waɗanda suke zāgayāwa, suna kēwaya gadon mulki sāfe da marēce.
Haka nē, ruwan kalmōmi yake zubōwa daga samāniyar ƙudirin Ubangijinka, mai rahama. Ku jākuɗo kusanta, yā ku al’umma, ku yi wātsi da waɗanda suke gardama ta wōfi da banza bisa āyōyin da Allah ya sauko, kuma da suka ƙi yarda da Ubangijinsu da ya zō musu ɗauke da hujja da shaida.
(Ayyam-i-Tis’ih shāfi 45-47)
Shīnē tsarkakakke, maɗaukaki, Mafi girma.
Cikin wannan watā nē, aka haifi wanda yake ɗauke da sūnā mafi girma, wanda bayyanarsa ta kāwo gilgiza ga duka al’ummōmin dūniya, wanda ƙūrar sāwunsa ta zama abun yabo ga majalasar samāniya da mazaunan birānen sūnāye. Dōmin wannan haifuwa, sai suka yi gōdiya ga Allah, suka yi gūɗa, kuma suka jī dāɗi matuƙa. Nā rantse da Allah! gā watan da ta garēshi nē duk watanni suka haskaka, watā da cikinsa nē wanda shīnē gaibu ɓōyeyye da ma’ādani tsararre ya bayyana, kuma ya ɗaga muryarsa cikin ƴan adam. Duka īkō nā hannun wannan jinjiri, da ta garēshi nē fuskar halitta ta sāmu hasken murmushi, itāce suka yi līlō, tēkuna suka kumbura, tsaunika suka tāshi, aljanna ta ɗaga murya, dūtsi ya yi kūwa, kuma sū duka suka cē : « Yā ku majalasar halitta ! ku tāshi ku nufi gabashin fuskar Ubangijinku, mai rahama, mai jinƙai ! ».
A cikin wannan watan nē, ita kanta aljanna ta sāmu ado da ƙyalƙyalin fuskar Ubangijinta, mai rahama, sūdar samāniya ta rēra wākarta bisa itāciyar Ubangiji, kuma zukācen gātāye suka ji dāɗi. Sai dai inā, yawancin mutāne ba su kula ba. Murna ta tabbata ga wanda ya yarda da Shi, kuma ya gāne da alkawalin dake cikin kitābin Ubangiji, mai īko, wanda shīnē abun yabo, kuma rūɗāni ya tabbata ga wanda ya jūwa bāya ga wanda majalasar samāniya ta kafa kallonta a garēshi, wanda ya ƙaryatar da kāfirai ɓatattu.
Idan ka sāmu wannan allō, ka wāƙe shi da iyākar zāƙin murya, kuma ka cē : Yā Ubangijīna mai rahama, yabo ya tabbata a garēka, da ka tuna da ni cikin wannan allō wanda ta garēshi ƙamshin rīgar saninka ya fitō, kuma ka malālō tēkunan alfarmarka. Nā shaida da cēwa, kana da īkon yin abun da ka ga dāma. Bābu wani Allah illā kai, mai īko, masanin kōmi da kōwa, mai hikima.
(Ma’idiy-i-Asmani kundi na 4 shāfi 342)
Wannan āyā, ana jan ta a ƙabarin Baha’u’llah, kō na Bab (tsīra da aminci su tabbata a garēsu). Wanda yake sō, yana iya karantā ta, rānēkun haifuwarsu.
Yabo dake dangance da zamantakēwarka mai martaba, kuma da mahibbar da ta haskō daga ƙyalƙyalin kyāwonka, su tabbata a garēka, yā kai da kai nē alāmar girma, da kai nē sarkin dawwama har abada, kuma da kai nē Ubangijin duk abūbūwan dake ƙasa da sammai !
Nā shaida cēwa, ta garēka nē, mulkin Ubangiji Allah, martabarsa da girmansa, suka bayyana, taurārun sāfiyar kyaukyāwar dauri, suka baza haskensu da bā ya shūɗēwa, cikin samāniyar kudurinka, kuma kyāwon wanda bā ya ganuwa, ya haske jiririn halitta.
Nā shaida kuma da cēwa, daga rubūtun alƙalaminka guda, sai umarninka « kasance » ya aikata, ɓōyeyyen gaibun Ubangiji Allah ya bayyana, ka rāya duka halittu, kuma duka wahāyi ya sauko.
Nā shaida cēwa, ta kyāwonka nē, kyāwon wanda shīnē abun yabo ya bayyana, kuma ta fuskarka cē, fuskar wanda shīnē abun ƙauna ta fitō hīli, kuma da kalmā guda, ka ƙayyada matsayin duk halitta, ka ɗaukaka wanɗanda suka yi īmāni har zuwa ƙōli, kuma ka jēfa kāfirai cikin rāmi mai zurfi.
Nā shaida cēwa, wanda ya amince da kai, yā amince da Allah Ubangiji Subahānahu wa ta āla, kuma wanda ya kai garēka, yā kai ga Ubangiji Allah. Albarka ta tabbata ga wanda ya yarda da kai kuma da alāmunka, ya gwada tawāli gaban martabarka, kuma ya sāmu sāduwa da kai, ya cinma bukātunka, ya jāƙuɗo kusanka, kuma ya durƙusa gaban karagarka.
Hallaka ta tabatta : ga wanda ya ɗauki zunubi garēka, ya yi wātsi da kai, ya yi jīfa da alāmunka, ya ƙi yarda da martabarka, kuma ya tāshi ya kai maka hari, ya gwada girman kai a gabanka, ya ƙi karɓar shaidōdinka, ya kēɓēwa dōkōkinka, ya yi adāwa da ikonka, ya shiga cikin kāfiran nan da sūnāyansu suke rubūce bisa tsarkakkun allunan ƙudurarka.
Daga dāmar rahamarka da alhērinka, ka sauko mani, yā Allah Ubangijina, abun ƙaunāta, tsarkakakkar bazarar alhērinka, dōmin ta ƙēɓē ni da nī kaina, kuma da dūniya, sabōda ta jāgōrancē ni wajen dandalin kusantarka da kaiwa garēka. Kana da īkon aikata abun da ka ga dāma, hakīka, kai nē bisa ga kōmi da kōwa.
Ambatar Ubangiji Allah, da yabonsa, ɗaukakarsa da girmansa su tabatta a garēka, yā kai wanda kai nē kyāwonsa ! Nā shaida da cēwa, bābu idon halittar da ya kalli wanda aka zālunta kamar kai. Duk rāyuwarka, an zunduma ka cikin tēkun rūdāni. A wani lōkaci, an ɗaure ka da sarƙa da mari, a wani lōkaci kuma, maƙiyyanka sun zāre maka takubbansu. Amma, duk da haka, kā gayyaci mutāne, da su bi umarnin da wanda shīnē al’alīmu, mai hikima maras iyāka, ya sauko a garēka.
Ina rokon Ubangiji, da ya karɓi rūhūna, tamkar tōshi, dōmin wahalōlin da ka gabāta, kuma ya amshi raina sabōda adāwar da aka maka. Ina roƙon ka, don darajarka da waɗanda fuskarsu ta sāmu ƙyalƙyalin hasken fuskarka, waɗanda don matuƙar ƙaunarka, suka karɓi duk abūbūwan da ka umarcē su da yi, ka kēta lābilen da ya raba ka da halittarka, kuma ka bā ni alhērin dūniya da na lāhira. A gaskiya, kai nē al’azīzu, kai nē al’alīyu, mafi ɗaukaka, mai gāfartāwa har kullun, mai jin-ƙai.
Yā Ubangiji Allāna, ka albarkatar da itāciyar Ubangiji, da ganyenta, da rassunta, da tsironta, da karanta, da ƴāƴanta, har iyākar tsawon sūnāyenka māsu martaba, da laƙanunka mafi ɗaukaka. Ka kāre su, da harin maƙiya, da rundunōnin azzālumai. A gaskiya, kai nē al’azīzu, al ƙādiru. Yā Allāna, ka albarkatar da bāyinka maza da māta, da suka isō garēka. A gaskiya, kai nē mai rahama, wanda alfarmarsa bā ta da iyāka.
Bābu wani Allah illa kai, mai gāfartāwa a kullun, mayalwaci.
Wannan āyā, ana jan ta a ƙabarin Abdul Baha, amma kuma mutun yana iya jan ta, don rāɗin kansa.
Idan kā yi wannan addu’a cikin īmāni da tawāli, haka nā sā zūciyar Abdul Baha ta jī dāɗi, kamar dai kana gabansa nē.
Shīnē Al majīdu.
Yā Allah, Allāna ! Cikin tawāli da sujāda, nā ɗaga hannuwāna wajenka, cikin rōko, kuma nā ɗōra gōshīna bisa ƙūrar balbālinka, wanda ya fi ƙarfin duk wani sanin masani da yabon duk abun da yake ɗaukaka sūnanka. Ka kalli da idon rahama, wannan ƙasƙantaccen bāwan nāka kāsashē, da yake gaban ƙōfarka, kuma ka zunduma shi cikin tēkun alfarmarka maras ƙārēwa.
Yā Ubangiji ! Gā bāwanka matalauci ƙasƙantacce, yana rōƙo cikin sūjada, kāme cikin hannunka, yana addu’a cikin armashi da yarda a garēka, idānuwansa cike da hawāye gaban fuskarka. Wannan bāwa, yana kiranka, yana rōƙonka da cēwa : « Yā Ubangiji Allāna, ka ƙarfafā ni cikin bautāta a garēka, ka haske gōshīna da hasken ibāda a cikin dandalinka mai tsarki, kuma da hasken addu’a cikin daularka mai girma. Ka taimakē ni, in yi wātsi da kōmi gaban dakalin ƙōfarka ta samāniya, kuma in dangana da kōmi a cikin balbālinka mai tsarki.
Yā Ubangiji, ka sā ni in shā cikin luddan dangana, ka sā mani rīgarta, kuma ka zundumā ni cikin tēkunta. Ka maida ni ƙūra bisa hanyar masōyenka, ka yardē mani in bāda tōshin raina ga ƙasar da ka darajanta da sāwun zāɓāɓɓu dake bin hanyarka, yā kai Ubangijin ɗaukaka cikin ɗaukaka.»
Ta wannan addu’a, bāwanka nā kiranka cikin assuba da dare. Ka ƙarɓi buƙātar zūciyarsa, yā Ubangiji ! Ka haskē, kuma ka sā murna cikin ransa, ka wāye rūhunsa, dōmin ya kyautatāwa umarninka da bāyinka.
Kai nē mayalwaci, mai jin-kai, mai karāma, mai rahama, mai kulāwa.