Return to BahaiPrayers.net
Facebook
Idan an zāɓi yin wannan salla, a bāyan an yi arwalla, a tāshi, a jūya gabā gabas maso arēwa, a dūbi dāma da hauni, tamkar mai nēman rahamar Ubangiji, ar-rahamane, mai jinƙai, kuma a cē :
Yā kai wanda kai nē Ubangijin duka sunāyē, kuma mahaliccin sammai ! dōmin darajar waɗanda sū nē asubāhin zātinka mai girma, ma fi ɗaukaka, da ya wuce a gāne Shi, ina rōƙon ka sā sallāta, ta zamana tamkar wutar da zā ta ƙōnē yānar dake hanā ni ganin kyāwonka, kuma ta haske hanyāta zuwa tēkun kusantarka.
A ɗaga hannuwa wajen Ubangiji, yabo da ɗaukaka su tabbata a garēshe, a cē:
Yā kai buƙātar dūniya, gātan duka al’umma, kana gani nā jūwa huskāta wajenka, cikin wātsi da duka wata dōgara ga kōwa in bā kai ba, kuma riƙe da igiyarka wadda mōtsinta nē yake mōtsa halitta gabāɗayanta. Yā kai Ubangijina, nī bāwanka nē, kuma ɗan bāwanka. Kana gani nā shirya cika ƙudurarka, kuma da abun da kake sō. Bā nā son kōmai, sai abunda kake sō.
Ta hanyar tēkun rahamarka da rānar alfurmarka, ina rōƙon ka ɗōrāwa bāwanka abun da kake sō, da ya dāce a garēka. Nā rantse da īkonka da ya wuce kwatamci da kirāri, duka abun da ka bayyana, shīnē gūrin zūciyāta da abun ƙaunar rūhūna.
Yā Allah Ubangijina, kada ka dūbi nufīna kō aikīna, amma ka dūbi īkonka wanda ya lulluɓe sama da ƙasa. Yā kai Ugangijin duka al’umma, da sūnanka mafi girma, bā na buƙātar kōmi, in bā abun da kake buƙāta ba, kuma bā nā son kōmi in ba abun da kake sō ba.
A durƙusa, kuma gōshi bisa ƙasa a cē :
Ɗaukakarka tā wuce duk wani kwatamci wanda bā nāka ba, kuma tā wuce fahimtar kōwa in bā tāka ba.
A tāshi, a cē :
Yā Ubangijina, ka maida sallāta marmaron ruwa garai da zā ya rāyar da ni har abada, kuma sallar nan, ta sā in ambacē ka cikin kōwace dūniyarka.
A tāshi, kuma a ɗaga hannuwa cikin rōƙo, a cē:
Yā kai da kake zāzafa zūkāce da rūhunnai idan sun nīsanta da kai, kuma da kake haske dūniya gabāɗayanta da hasken sōyayyarka! Da sūnanka mai sanyaya duka ran halitta, ina rōƙon kada ka hanā mani duka abun da yake nāka, yā kai mai īkon duka ƴan adam! Yā Ubangijina, kanā ganin wannan bāƙon yana gaugautāwa wajen mabartarsa mafi ɗaukaka, ƙalƙashin runfar martabarka, gaban bangon rahamarka, wannan mazunubanci da yake nēman tēkun gāfararka, wannan ƙasƙantacce da yake zuwa nufa fādar ɗaukakarka, wannan miskīni da yake nēman arzikinka.
Kai kake umurta abun da kake sō! Nā shaida cēwa, yabo yā cancanca ga duka ƙudurarka da abun da ka aikata, kuma cikkaken ƴinci yā tabbata ga dokokinka.
A ɗaga hannuwa, a jā “Allah’u’Abha” sau uku. A dūƙa gaban Ubangiji (albarka da yabo su tabbata a garēshi), a ɗōra hannuwa bisa gwiwōwi, a cē :
Yā Allāna, kana ganin yanda dukāna nake cike da buƙātar yabonka, da kuzārin kiran sūnanka, kuma da yaba ka; kana ganin yadda rūhuna yake fadaƙar da abun da harshen dōkarka ya ƙayyada cikin daular kalmarka, kuma bisa samāniyar iliminka. Yā Ubangijina, cikin wannan hālin da raina yake, ina ƙaunar tambayarka duka abun dake nāka nē, tunda nī maskīni nē, ina ɗaukaka alhērinka da arzikinka, tunda nī talakka nē, ina tabbatar da īkonka da ƙarfinka.
A mīƙe, kuma a ɗaga hannuwa sau biyu, a rōƙi cēwa:
Bābu wani Allah sai kai, mai ƙudura, mai yalwā maras iyāka. Bābu wani Allah sai kai, ma’umurcin farko da na ƙarshe. Yā Ubangiji Allāna, afuwarka tā bāni kuzāri, kuma rahamarka tā ƙarfafa ni; kiranka yā falkar da ni, alfurmarka tā ɗaga nī zuwa garēka. Idan bā haka ba, ta yāya zā ni tarki tsayāwa ƙōfar fādarka, kō kuma in ɗaga fuskāta wajen hasken dake ƙyalƙyali daga samāniyar ƙudurarka ?
Yā Ubangijina, kana ganin wannan miskīni yana ƙyarƙyara ƙōfar alfurmarka, wannan rūhu nā nēman ƙōramar rāyuwar har abada, daga cikin hannun yalwarka.
Yā kai Ubangijin duka sunaye, īko yana garēka kōwane lōkaci, nī kuma haƙuri da ladabi ga ƙudurarka, sū nē nāwa, yā mahaliccin sammai !
A ɗaga hannuwa sau uku, a cē:
Allah shīnē mafi girma!
A ɗurƙusa goshi a ƙasa, a cē :
Ɗaukakarka tā wuce matsayin da yabon māsu kusantaka da kai, ya isa samāniyar fadarka, kō tsuntsāyen zūkācen masōyanka su kai ƙōfarka.
Nā shaida cēwa, tsarkakarka tā wuce kōwane laƙani da kōwane sūna. Babu wani Allah sai kai, mai mulki, maɗaukakin sarki.
A zauna a cē :
Kamar duk halittu, malā’ikun samāniya, mazaunan aljannar ƙōli, kuma sama da su, mazaunan sararin samāniyar ɗaukaka, da harshen martaba shi da kansa, nā shaida cēwa, kai nē Allah, bā ka da abōkin tārayya, kuma wanda ka manzonta shīnē, bōyeyyen gaibu, shīnē alāma mai daraja. Ta garēshi aka haɗa baƙaƙe k-a-s-a-n-c-e (kasance), kuma aka haɗā su, aka ɗaure su.
Nā shaida cēwa, sūnansa nē alƙalamin ƙudura da irāda ya rubuta, kuma aka ambata cikin litattafan Allah Ubangijin karagun sama da ƙasa.
A tāshi a cē :
Yā kai Ubangijin duk halitta, kuma mamallakin duka abūbūwan da ake gani kō dake ɓōye, kana ganin hawāyēna, kana jin nīshīna, kana jin kūkāna, gungunīna da takaicin dake zūciyāta. Don girmanka, laifuffukāna suna hana ni kusanta da kai, kuma zunubaina, nā nīsantā ni da tsarkakarka.
Yā Ubangijina, ƙaunarka nā arzitar da ni, rabuwa da kai nā hallakā ni, kuma nīsanta da kai, nā tōya ni rumus. Da sūnan sāwunka cikin hamāda, ta wannan kalmōmi «gā ni, gā ni !» da gātāyanka suke faɗa cikin sarari, da sūnan numfāshin bayyanarka, da iskar sāhiyar wahayinka, ina rōƙon ka yarda, in kalli kyāwonka, kuma in bi duka abun dake cikin kitābinka.
A jā Allah’u’Abha sau uku, a ɗūka, hannuwa bisa gwīwōwi a cē :
Yabo ya tabbata a garēka yā Allāna! kana taimako nā da tunāni da kai, kuma da yabāwa da kai. Kana sanarshe ni da wanda shīnē assubāhin āyōyinka. Kana sā ni dūƙāwa gaban īkonka, durƙusāwa gabanka, kuma da yarda da abunda harshen girmā ya ayyana.
A tāshi, a cē :
Yā Allah Ubangijina, nauyin zunubaina yā sā na yi dōro, kuma sakacīna yā hallakā ni. Idan na yi nazari bisa laifufukāna da alhērinka, zūciyāta sai ta kātse, jikīna ya yi sanyi. Yā kai abun shāwar duka dūniya, dōmin kyāwonka, sai na ji kunyar ɗaga fuskāta wajenka, kuma na ji kunyar ɗaga hannuwāna, dōmin rōƙo wajen samāniyar alhērinka.
Yā Allāna, kana ganin yanda hawāyēna suke hana mani ambatar ka da yaba iyāwarka, yā kai Ubangijin karagun sama da ƙasa! Don sabōda alāmun īkonka, kuma da gaibun daularka, ina rōƙon, ka dūbi masōyanka da idon alfurmarka, yā kai sarkin abūbūwan da ake gani da na ɓōye.
A jā Allah’u’Abha sau uku, a durƙusa, gōshi a ƙasa a cē :
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allah! Kana bayyana muna abun da yake kusantar mu da kai, kuma kana bā mu duka alhērin dake cikin litattafai da kitābōbinka.
Yā Ubangijinmu, muna rōƙon ka kāre mu da rundunar tunāninmu na wōfi, da ra’āyōyinmu na shirme. A gaskiya, kai nē mai ƙudura, masanin kōmi.
A tāshi tsaye a ce:
Yā Allāna, nā shaida abūbūwan da gātāyanka suka shaida, kuma nā faɗakar da abun da mazaunan aljanna, da waɗanda suke kēwaye da karagar fādarka, suka faɗakar. Daulōlin ƙasa da na sama duka nāka ne, yā Ubangijin dūniyōyi.
- Bahá'u'lláh