Return to BahaiPrayers.net
Facebook
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allāna! Kai nē wanda daga būɗa bāki, sai duka dūniya ta yi gilgiza, wanda daga kurta alƙalaminka, ka rarraba bāyunka. Nā shaida yā Allāna, da cēwa, a wannan wahayi, kalmarka guda ɗaya tā sā duk halitta tā zama mai hallaka, kuma da wata kalmar, duk wanɗanda ka zāɓā, suka rāyu da sābuwar rāyuwa, dōmin alfurmarka da karāmarka. Sabōda haka, nike maka gōdiya da yabo, don darajar duk waɗanda kake ƙauna, waɗanda ka sāke rāyāwa da ruwa māsu rāyarwa, da suka ɓullo daga marmaron yardarka.
Tunda yake, kā rāyar da su a cikin alhērinka mai girma, yā Allāna, ka sā hankalinsu ya kōma zuwa wajen umurninka. Da yake kā yarde musu, shiga cikin ɗākin addīninka, ka yarde musu a cikin alfurmarka, kada kōmi, ya riƙe su nēsa da kai. Ka būɗe mā zukācensu yā Allāna, ƙōfōfin saninka, don su gāne da kai nē wanda ya fi a gāne shi, wanda duk halitta ba ta isa ta farga da iyākacinsa ba, wanda yake yā wuce inda, kōmin ƙōƙarin bāyinka, su fahimta da yanda kake ciki, kuma ka wanke zukācensu, dōmin kada su kula da waɗannen maƙaryata, māsu yawan sūrūtu da suke ƙariyar batu da sūnanka.
Yā Ubangijina, ka bā bāyin nan nāka, hamzarin da zā su sarkafa a addīninka da kuzāri ta yanda har abada, bā zā su kula ba da habaicin wanɗanda ba su sā kōmi gaba ba, in bā abun dūniya ba, masu aikata abūbūwan da ka hana a cikin litattafanka da kitābanka. Kā san yā Allāna, ina jin kūkan kūrāyen da suke bayyana da kamannin bāyinka. Ka kāre masōyanka da sharrinsu, kuma ka yarda su riƙe abin da ka bayyana cikin wanan wahayi nāka wanda cikin saninka, ka ƙayyada cēwa, bā shi abōkin tārayya.
Ka isar musu, yā Allāna, da abun cin mōriya, ka haske su da hasken saninka don su fahimta da kai nē sama ga kōmi, kuma su shaida da ɗaukakarka a bisa halittarka da nasararka ga waɗanda suke sama da na ƙasa. Ka na da īkon aikata kōmi, yanda ka ga dāma. Bābu wani Allah in ba kai ba. Kai nē jalla, wanda duk tāliki yake rōƙon taimakonka.
Yabo ya tabbata a garēka, yā kai Ubangijin tālikai.
- Bahá'u'lláh