Return to BahaiPrayers.net
Facebook
Wannan āyā, ana jan ta a ƙabarin Abdul Baha, amma kuma mutun yana iya jan ta, don rāɗin kansa.
Idan kā yi wannan addu’a cikin īmāni da tawāli, haka nā sā zūciyar Abdul Baha ta jī dāɗi, kamar dai kana gabansa nē.
Shīnē Al majīdu.
Yā Allah, Allāna ! Cikin tawāli da sujāda, nā ɗaga hannuwāna wajenka, cikin rōko, kuma nā ɗōra gōshīna bisa ƙūrar balbālinka, wanda ya fi ƙarfin duk wani sanin masani da yabon duk abun da yake ɗaukaka sūnanka. Ka kalli da idon rahama, wannan ƙasƙantaccen bāwan nāka kāsashē, da yake gaban ƙōfarka, kuma ka zunduma shi cikin tēkun alfarmarka maras ƙārēwa.
Yā Ubangiji ! Gā bāwanka matalauci ƙasƙantacce, yana rōƙo cikin sūjada, kāme cikin hannunka, yana addu’a cikin armashi da yarda a garēka, idānuwansa cike da hawāye gaban fuskarka. Wannan bāwa, yana kiranka, yana rōƙonka da cēwa : « Yā Ubangiji Allāna, ka ƙarfafā ni cikin bautāta a garēka, ka haske gōshīna da hasken ibāda a cikin dandalinka mai tsarki, kuma da hasken addu’a cikin daularka mai girma. Ka taimakē ni, in yi wātsi da kōmi gaban dakalin ƙōfarka ta samāniya, kuma in dangana da kōmi a cikin balbālinka mai tsarki.
Yā Ubangiji, ka sā ni in shā cikin luddan dangana, ka sā mani rīgarta, kuma ka zundumā ni cikin tēkunta. Ka maida ni ƙūra bisa hanyar masōyenka, ka yardē mani in bāda tōshin raina ga ƙasar da ka darajanta da sāwun zāɓāɓɓu dake bin hanyarka, yā kai Ubangijin ɗaukaka cikin ɗaukaka.»
Ta wannan addu’a, bāwanka nā kiranka cikin assuba da dare. Ka ƙarɓi buƙātar zūciyarsa, yā Ubangiji ! Ka haskē, kuma ka sā murna cikin ransa, ka wāye rūhunsa, dōmin ya kyautatāwa umarninka da bāyinka.
Kai nē mayalwaci, mai jin-kai, mai karāma, mai rahama, mai kulāwa.
- `Abdu'l-Bahá