*A cikin Kitābil Akdas, Ubangiji yā cē : ‘’Mun umurci mutun da yin azumi da zāran yā kai shēkara gōma shā biyar. Wannan umurnin Allah nē, Ubangijinku da Ubangijin uwāyenku. Māsu balāguro, marassa lāfiya, da māta masu jūnā biyu, kō māsu bāda nōnō, ba a umurce su da yin azumi ba. Idan kuna azumi, kada ku shā ruwa, ko ku ci abinci daga fitōwar rānā, zuwa fāɗuwarta, kuma kada ku yarda nishāɗi ya hana ku sāmun wannan ni’ima da aka rubūta a cikin littāfi. Ana azumi daga cikin watan Ālā.
Yā Allāna, don darajar āyarka mai ƙarfi, kuma da wahayin zuwa ga ƴan adam, ina rōƙon kada ka rufe mani ƙōfar birnin kasancewarka, kuma kada ka kunyata gūrīna da na sarƙafa ga bayyanar falalarka tsakānin halittunka.
Kana gani nā, yā Allāna, ina sarƙafe ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar muryarka mai zāƙi, kuma da maganarka mai girma, ina rōƙon ka jāwo ni kusa da dakalin ƙōfarka, kuma kada ka riƙe ni nēsa da inuwar rahamarka, kō zauren yalwarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, gaban kyaukyawar huskarka, kuma da kansancēwarka dake wātsa haske daga jiririn samāniyar ƙōli, ina rōƙon ka jāwo ni, in ji ƙamshin turāren tufāfinka, kuma ka bā ni dāmar jin maganarka mai zāƙi.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, dōmin gāshinka dake shāre fuskarka, da al’ƙalaminka maɗaukaki da yake rubūtu bisa shāfin āyōyinka, yana baza ƙamshin turāren muskin ɓōyayyun fusā’ō’i. Ina rōƙon ka taimakē ni, in kyautatāwa addininka, bā tāre da kāsāwa ba, kuma habaicin waɗanda suke adāwa da āyōyinka, kō suka juyāwa fuskarka bāya, su kāsa dabaibaye ni.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar sūnanka da ka naɗā shīnē, sarkin sūnāye, da yake ƙarfafa duk waɗanda ke sama da ƙasa, ina rōƙon ka bā ni ƙarfin tsinkāyar rānār kyāwonka, kuma ka zubo mani zaƙamin maganarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar tantin martabarka dake kafe a ƙōlōluwa mafi tsayo, kuma da zauren wahayinka dake bisa tudunnai mafi tsayi, ina rōƙon ka taimake ni da yalwarka don in aikata abunda nufinka yake buƙāta, da abunda shariɗōɗinka suka bayyana.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar kyāwonka mai haske a sararin dūniya na har abada, kyāwo wanda daga ɓullōwarsa daular kyāwo da kanta take masa sūjada, kuma take ɗaukakāwa da babbar murya. Ina rōƙon ka taimake ni, in rabu da duk abūbūwan da garēni, kuma in rāyu da abunda yake nāka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar bayyanar sūnanka, wanda shīnē abun ƙauna, wanda ya sā zukātun mumminai suka ƙōne da wutar sōyyaya, kuma ya sā rāyukan mazaunan dūniya suka haye wajensa. Ina rōƙon ka tallafē ni, in tuna da kai cikin halittunka, kuma in yabā ka cikin al’ummarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hannyar ƴāƴar iccen ɗaukakarka, da būsāwar bazarar sanyin bayyanarka cikin daular sūnāyenka, ina rōƙon ka nīsanta ni da abunda kake ƙyāma, kuma ka jāwo ni kusa da wurin da sahiyar alāmunka ta ɓullo.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar wannan baƙi, wanda daga fitōwarsa daga bākin irādarka, ya sā tēkuna suka kumbura, iska ta būso, ƴaƴan itāce suka fito, itātuwa suka tsiro, ya shāfe tsōfōfin ajjiya, ya kēce duk wani lulluɓi, kuma ya gaugauta mumunai wajen hasken fuskar Ubangijinsu mai ƴanci. Ina rōƙon ka sanarshe ni da abun dake ɓōye cikin zurfin arzikin iliminka da asūssun hikimarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar wutar sōyyayarka da take kōre kwāna daga idānuwan zāɓɓaɓun bāyunka da masōyanka, kuma dōmin ambatarka da suke tun assuba. Ina rōƙon ka sā ni cikin sahun waɗanda suka kai ga abun da ka bayyana cikin kitābinka, kuma ka ƙayyada cikin irādarka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafe ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar hasken kasancēwarka da take sā māsu ƙaunarka su gabāci kibiyōyin ƙudurarka, kuma ta sā mabiyanka su fuskanci takubban maƙiyanka, cikin hanyarka. Ina rōƙon ka bayyana mani, abun da alƙalaminka mai tsarki ya bayyanāwa aminnanka da zāɓāɓɓun bāyunka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
Yā Allāna, ta hanyar sūnanka dake saurāren kiran masōyanka, da ajjiyar zūcin waɗanda kē ƙaunar ka, da kūkan waɗanda suke kusa da kai, da nīshin mabiyanka, ta hanyar sūnanka da yake cinma gūrin waɗanda suka danganta da kai, suke kai ga jin dāɗinsu ta wajen alfurmarka da yalwarka, ta hanyar sūnanka dake sā tēkun gāfartāwa ya zāburo gaban fuskarka, kuma kyautarka ta zubo bisa māsu bautā maka. Zuwa ga duk waɗanda suka jūya wajenka, suna yin azumin da ka umurcē su da yi, ka rubūta lāda ga wanɗanda bā su magana sai da izininka, kuma suka yi wātsi da duka abūbūwan da garēsu, dōmin ƙaunarka bisa hanyarka.
Ta hanyarka da alāmu da hujjōjinka, ta hanyar hasken rānar kyāwonka da rassunka, ina rōkon ka shāfe laifin waɗanda suke bin dōkōkinka, suna yin abūbūwan da ka umurcē su da yi cikin kitābinka.
Kana gani na, yā Allāna, ina sarƙafē ga sūnanka, mafi tsarki, mafi haske, mafi īko, mafi yabo, mafi ɗaukaka, kuma ina riƙe da sāshen rīgarka da kōwa yake kāmāwa dūniya da lāhira.
- Bahá'u'lláh
Yabo ya tabbata a garēka yā Ubangiji Allāna. Ina rōƙon ka, don darajar wannan bayyana, da ta maida duhu haske, kuma da garēta a ka gina masallacin jama’a, da garēta kuma aka sauko rubutaccen allo, a ka shinfida ɓoyayyan kundi, ina rōƙon ka sauko mana, ni da abōkan zamāna, abun da zai sā mu hira wajen samāniyar ɗaukakarka, kuma abun da zai tsarkakar da mu da dauɗar shakka da ta hana waɗanda ba su amince ba, shiga cikin zauren ɗayantakarka. Yā Ubangijina, gā ni, nī nē wanda ya sarƙafu ga igiyar alfurmarka, kuma ya rātayu ga zanen rahama da alhērinka. Ka zubo mana ni da duk waɗanda nike ƙauna, albarkan nan da ka wārewa zāɓaɓɓun bāyunka.
Yā Ubangijina, ga rānaikun da ka umurci bāyunka da ɗaukan azumi. Albarka ta tabatta ga wanda ya ɗauki ƙishurwa, kawai sabōda ƙaunarka, kuma cikin wātsi da kōmi in ba kai ba. Ka taimakē ni kuma ka tamaike su, yā Ubangijina, don mu bi umurninka, kuma mu tsaida dōkōkinka.
A gaskiya ka nā da īkon yin abin da ka ga dāma. Bābu wani Allah illā kai, mafi sani da basīra. Dukan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin duka dūniya.
- Bahá'u'lláh