Yā kai ɗan rūhu !
Gargaɗīna na farko shī nē : Zūciyarka ta zama fara ƙal, mai yalwa, mai haske, dōmin ka sāmu babban ƴanci na tun fil azal, maras ƙārēwa har abada.
Yā kai ɗan rūhu,
A garēni abu mahi kiyāwo shī nē ādalci, kar ka yi nīsa da shi, idan dai nī kake ƙauna, kuma kar ka yi sake da shi sabōda in bā ka yardāta.
Ta wannan hanyar cē, zā ka iya gani da idānuwanka, bā da na waɗansu ba, zā ka iya fahinta da iliminka, bā da na wani ba.
Tunā da kyau : ƙāƙā ya dāce ka zamana ? a gaskiya, ādalci shī nē kyautar da na yī maka, shī nē shaidar alhērina zuwa garēka. Kar ka dēna yin la’akari da shi.
Yā kai ɗan Adam
A ɓōye cikin rāyuwāta wadda ta wuce tunāni, kuma cikin haƙiƙantaccen aināfin usilīna, nā yi sanin sōyayyāta zuwa garēka, don haka nē na haliccē ka. Na sā kamannuna a garēka, kuma na bayyanā maka kyāwōna.
Yā kai ɗan Adam,
Nā sō halittarka, don haka nē na haliccē ka. Kēnan ka iya ƙaunā ta, dōmin in ambaci sūnanka, kuma in cika kurwarka da rūhun rāyuwa.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Gwadā mini ƙauna don in sō ka. Idan dai bā kā ƙauna ta, bā yanda sōyayyāta zā ta isa garēka. Ka san da wannan, yā kai tāliki.
Yā kai ɗan rāyuwa,
ƙaunāta ita cē aljannarka, sāduwa da ni shī nē mazauninka na samāniya. Gaggauto zuwa garēta. Wannan shī nē umurnin da muka ƙayyade maka daga daularmu ta samāniya, kuma cikin mulkinmu na ƙōli.
Yā kai ɗan Adam,
Idan kanā ƙaunā ta, ka dēna kulāwa da kanka, idan kuma kanā buƙātar dāɗin raina,
kada ka tuna da nāka, dōmin ka cika bauta mini, nī kuma in bayyana kullum a garēka.
Yā kai ɗan rūhu,
Bābu wata kwanciyar hankali a garēka idan dai ba ka manta da kanka ba, kuma ka jūya hankalinka wajēna; lalle yā cancanta ka yi yabon kanka da sūnāna bā da nāka ba, ka bā ni amāna bā ka bā kanka ba, don nā fi da son a ƙaunacē ni, nī kaɗai, kuma hiye da kōmi.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Ƙaunāta ita cē gārūna, duk wanda ya shiga ciki, yā tsīra, kuma yanā cikin kwanciyar hankali, duk wanda ya kauce kuwa, bā shakka zai ɓata, kuma yā hallaka.
Yā kai ɗan furuci,
Kai nē gārūna, ka shiga cikinshi don ka sāmu rāyuwa cikin kwanciyar hankali. Ƙaunāta tanā a garēka, ka san da haka dōmin ka kusancē ni.
Yā kai ɗan rāyuwa
Kai nē fitilāta, kuma haskēna nā dashe a garēka. nēmō nāka hasken a garēshi, kuma kada ka buƙāci kōwa in bā nī ba. Tunda dai nā halicce ka da arziki, kuma a bisanka, na barbaɗa alfurmāta.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Da hannuwan īkō, na yi maka siffa, kuma da yātsōtsin ƙudura na halittō ka; kuma a garēka na dasa tūshen haskēna.
Ka iya dangana da haka, kuma kada ka nēmi kōmi, sabōda hikimāta ita cē muhimmiya, kuma umarnīna yā tilasta ka da yin haka. Kada ka yi zato kō shakka.
Yā kai ɗan rūhu,
Nā halicce ka mai arziki, yāyā kake maida kanka matsiyāci? Nā yī ka mai daraja, yāyā kake ƙasƙanta kanka? Nā rāya ka da tūshen sani, yāyā kake nēman haske ga wani? Nā ƙēra ka cikin yumɓun ƙauna, yāyā kake kulāwa da wani bā nī ba? Jūyō kallonka wajenka, kanā gani nā hallara a garēka, Mai ƙarhi, Mai ikō kuma Mabuwāyi.
Yā kai ɗan adam
Kai nē dūkiyāta, dūkiyāta kuwa bā ta ƙārēwa; kēnan don mi kake tsōron mutuwa? Kai nē haskēna, haskēna kuwa har abada, bā yā biccēwa, yāyā kake tsōron suƙēwa? Kai nē ɗaukakāta, ɗaukakāta kuwa bā ta shāfēwa; kai nē rīgāta, rīgāta kuwa bā tā tsūfā har kullum. Ka ƙarfafa kaunarka a garēni, dōmin ka sāmē ni cikin daular ɗaukaka.
Yā kai ɗan furuci,
Juyō huskarka wajen tawa kuma ka yi wātsi da kōmi ban da ni, sabōda mulkīna madawwami nē, kuma daulāta bā ta da iyāka. Idan wani kake nēma bā nī ba, haƙiƙā, kō da zāka bincika dūniya dīman, bincikenka bā zā ya dāce ba.
Yā kai ɗan haske,
Manta da kōmi in bā nī ba, kuma ka nēmi sāduwa da rūhūna. Wanan shī nē tūshen umarnīna, kēnan ka bī shi.
Yā kai ɗan Adam
Ka iya dangana da ni, kuma kada ka nēmi wani macēci illā ni, sabōda har abada bā wani mai iya isar ka, in bā nī ba.
Yā kai ɗan rūhu,
Kar ka tambayē mu abun da bā mu buƙātar ka da shi; ka yi farin ciki da abun da muka tānadar maka na alhēri, sabōda haka nē mafi amfāni a garēka, idan kai mai dangana nē da wannan.
Yā kai ɗan muhimmin gani,
Nā busa rūhūna a garēka don ka kasance amīnīna. Yāyā kake sakī na ka nēmi wani masōyi daban da ba nī ba?
Yā kai ɗan rūhu,
Hakīna a garēka yanā da girma, yā fi ƙarfin a manta da shi. Alfurmāta a garēka bā ta da iyāka; tā fi ƙarfin a lulluɓē ta. Ƙaunāta tā maida ka mabartarta, tā fi ƙarfin a ɓōyē ta. Haskēna yā zama gananne a garēka, yā fi ƙarfin a duhuntā shi.
Yā kai ɗan Adam,
A bisa itāciyar ɗaukaka, nā rātaya maka zāɓaɓɓun ɗiyā; don mi kake wātsi da su ka kuma dangana da waɗanda ba su kai dāɗinsu ba? Tō dāwō wajen abun da ya fiyē maka cikin daular samāniya.
Yā kai ɗan rūhu,
Nā haliccē ka da darajarka, ammā kā ƙasƙanta kanka. Tō, ɗaukaka kanka ga matsayin halitarka.
Yā kai ɗan mafi girma,
Ina kiran ka zuwa ga rāyuwa ta har abada, ammā kai kanā nēman abu mai ƙārēwa. Yāyā kake wātsi da bukātarmu kake nēman tāka bukāta?
Yā kai ɗan Adam,
Kar ka wuce matsayinka, kuma kar ka tambayi abun da bai dāce ba a garēka. Yi sūjada a gaban fuskar Ubangijinka, sarkin ƙudra da irāda.
Yā kai ɗan rūhu,
Kada ka yi fankama gaban matalauci, sabōda nī nike masa jāgōra, don ina ganin ka cikin hālin ashsha, kuma inā kumnyatā ka har abada.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Yāyā kake mancēwa da nāka laifukan, ka kula da na waɗansu? Duk mai aikata haka, nā la’ance shi.
Yā kai ɗan Adam,
Kar ka furta zunuban wasu, tunda kai mā mai aikata zunubi nē. Idan dai ka ƙētara wannan umurnin, la’anna zā ta tabbata a garēka, kuma nā shaida da haka.
Yā kai ɗan rūhu,
Ka san da haƙiƙan cēwa, duk wanda yake umurtar ƴan adam da yin ādalci, kuma shi da kansa yake rishin ādalci, bai gādē ni ba, kō dā yanā ɗauke da sunāna.
Yai kai ɗan rāyuwa.
Kar ka zargi kōwa da abun da ba zā ka sō a zargē ka da shī ba, kuma kar ka faɗi abun da ba ka aikata ba. Wannan shī nē umurnīna a garēka, ka kiyāye da shi.
Yā kai ɗan Adam,
Kar ka hanāwa bāwāna abun da zā ya iya tambayar ka, sabōda fuskarshi fuskātā cē ; kēnan, kar ka zamana tsagērā a wajēna.
Yā kai ɗan rāyuwa.
Ka bunciki kanka da kanka kōwace rāna kāfin a kirāye ka ranar ƙiyāma : sabōda mutuwa zā ta zō maka bā tāre da tā shaida maka ba, kuma zā a tambayē ka bāda lābārin abūbuwan da ka aikata.
Yā kai ɗan Maɗaukaki,
Nā aikō maka mutuwa, dōmin ta zame maka sāƙon murna. Tō, don mi kake dāmuwa? Nā yi haske don ya haskake ka da ƙyalƙyalinsa. Don minēnē kake lulluɓēwa gabansa?
Yā kai ɗan rūhu,
Ta hanyar haskakkun lābāru na farin ciki, na yi kiranka ka yi murna. Na gayyace ka zuwa fādar tsarkaka, ka tsaya cikinta kō kā sāmu rāyuwa cikin lumāna har kullum.
Yā kai ɗan rūhu,
Rūhun tsarkaka yā kāwō maka kyaukyāwan lābāri na sāduwa; tō don mi kake ɓāta rai?
Rūhun mulki yā tabbata ka cikin addāninsa, don mi kake gōcēwa? Hasken fuskarshi nā gwada maka hanya; ta yāyā zā ka iya ɓacēwa?
Yā kai ɗan Adam,
Kada ranka ya ɓāci in bā lalle kanā nēsa da mu ba. Kar ka yi murna in bā lalle kā kusancē mu ba.
Yā kai ɗan Adam,
Ka yi murna a cikin zurfin zūciyarka, kō kā sāmu matsayin kusanta da ni, kuma kyāwōna ya tabbata gananne a garēka.
Yā kai ɗan Adam,
Kar ka tūɓe rigāta mai kyāwon gaske, kuma kar ka hana kanka rabonka a mashāyāta mai ban māmāki, dōmin gudun ƙishurwa har abada.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Ka bi ƙa’idōdina sabōda ƙaunāta, ka kuma yi wātsi da buƙātunka idan lalle kanā biɗar murnāta.
Yā kai ɗan Adam,
Kar ka yi sakaci da dōkōkīna idan kanā shāwar kyawōna, kuma kar ka manta da galgaɗīna idan dai kanā buƙātar jin dāɗīna.
Yā kai ɗan Adam,
Kō dā zā ka zābura ka gama sararin samāniya, ka kuma yi shāwāgi cikin duka fāɗin halitta, bā zā ka sāmu hūtū ba idan dai ba ka bi dōkōkinmu ba, idan kuma ba ka ƙasƙanta kanka gabanmu ba.
Yā kai ɗan Adam
Ɗaukaka addīnīna don in bayyana maka sirrīn girmāna, kuma in haske ka da haske na har abada.
Yā kai ɗan Adam,
Ƙasƙanta kanka gabāna don in tarbe ka da marhaba. Tāshi tsaye don cī gaban addīnīna, don ka sāmu nasara tun kanā dūniya.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Ka ambacē ni cikin dūniyāta, don in tuna da kai a samāniyāta, ta haka nē idānuwana da nāka zā su mōre.
Yā kai ɗan gadon sarauta,
Kunnuwanka kunnuwānā nē, saurarā da su. Idāduwanka idānuwānāna nē, da su zā ka yi kallō don ka shaida a cikin zurfin zūciyarka da muhimmiyar tsarkakāta, sai kuma nī mā, in shaida maka matsayi mai muhibba.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Nēmi mutuwar shuhāda bisa hanyāta, cikin jin dāɗi na murādīna, kuma cikin gōdiya da ƙudirīna, a lōkacin nan zā ka iya hūtāwa tāre da ni kusan kujērar martaba, bāyan fādar ɗaukaka.
Yā kai ɗan Adam,
Tunā kuma ka yi nazari. kanā buƙātar mutuwa bisa gadonka, kō kuma kā fi son zubda jininka cikin ƙūra, shāhīdi bisa hanyāta, don ka zamana kai nē dōkāta, kuma mai gwada haskēna cikin al’janna ta ƙōli? Ka yi shāwarar da ta kamāta, yā kai bāwāna.
Yā kai ɗan Adam,
Nā rantse da kyāwōna! Rina gāshinka da jininka abu nē wanda a garēni zā ya fi ƙīrar halitta gabāɗayanta da kuma hasken dūniya da lāhira. Ƙōƙarta ka cika wannan umurnin, yā kai bāwā.
Yā kai ɗan Adam
Kōwane abu yanā da alāmunsa. Alāmun sōyayya shī nē, dauriya a game da ƙudirōrina, kuma haƙuri a game da gwajīna.
Yā kai ɗan Adam
Masōyin gaske nā nēman wahala matuƙa kamar yadda kāfiri kē nēman gāfara, kuma mai sāɓō kē nēman jinƙai.
Yā kai ɗan Adam,
Idan wahala ba ta sāmē ka ba bisa kan hanyāta, yāyā zā ka iya bin sāwun waɗanda suke farin ciki da jin dāɗīna?
Idan wahala ba ta sāmē ka ba cikin ƙōƙarinka na nēman sāduwa da ni, yāyā don kaunar kyāwōna, zā ka sāmu dāmar isā inda haskēna yake?
Yā kai ɗan Adam,
Duk balā’in da ya fitō daga wajēna, ƙadarata cē; ka nā ganin alāmun wuta cē kō kisan gilla, alhāli kuwa, haskē nē da rahama. Gaggauto zuwa wajenta don ka iya zama haske na kullum, kō kuma rūhu madawwami. Wannan shī nē umarnīna, ka iya la’akari da shi.
Yā kai ɗan Adam,
Idan wadāta ta samu, kar ka yi murna; kuma idan wulāƙanci ya zō maka, kar ka dāmu, sabōda wannan duka māsu wucēwa nē su kuma shūɗē.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Idan talauci yā māmaye ka, kar ka dāmu, sabōda idan wa’adin yā kai, Ubangijin arziki zā ya zō a garēka. Kar ka ji tsōron wulaƙanci, tun da wata rānā ɗaukaka nā tabbata a garēka.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Idan zūciyarka nā hangen daula maras iyāka, kuma idan ta sarƙafa da wannan rāyuwa ta tun fil azal wadda bā ta ƙārēwa har abada, tō ka yi wātsi da duk wata martaba mai gajēren zāmani, kuma mai macēwa.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Kar ka kula da wannan dūniyar, sabōda ka san da cēwa: da wutā muke jinjina zīnāriya, hakanan kuma da zīnāriya muke gwajin bāyinmu.
Yā kai ɗan Adam,
Kai, ka na biɗar zīnāriya, Nī kuma inā buƙātar ka yi nīsa da ita. kanā tsammānin sāmunta shī nē arziki, nī kuma nā san da cēwa: rabuwa da ita shī nē arzikinka. Nā rantse da rāyuwata! Wannan shī nē sanīna, kuma shī nē jahilcinka. yāyā ra’ayīna da nāka zā su iya daidaituwa?
Yā kai ɗan Adam,
Rarraba dūkiyāta ga matalautāna don ka sāmu rumbun tsayayyar albarka a cikin samāniya, kuma da arzikin ɗaukaka maras ƙārēwa. Nā rantse da rāyuwāta! Bāyar da ranka shī nē abu mafi ɗaukaka, idan dai kanā iya gani da idānūna.
Yā kai ɗan Adam,
Ɗākin ibādar ɗan adam shī nē kujērar mulkīna; tsarkakē shi da duk wata dauɗa dōmin in sāmu girka mazaunīna.
Yā kai ɗan rāyuwa,
Zūciyarka gidāna nē; tsarkakē ta dōmin in sāmu sauka. Rūhunka shī nē wurin bayyanāta; tsarkake shi dōmin in bayyana.
Yā kai ɗan Adam,
Ƙāma tsatsōna ka ɗagā ni don in yi sama a garēka cikin murna da ƙyalƙyali.
Yā kai ɗan Adam,
Ɗaukaka kanka zuwa samāniyāta, dōmin samun murnar sāduwa da ni, da kuma sāmun shan muhimmin ruwan mōɗar ɗaukakā maras ƙārēwa.
Yā kai ɗan Adam,
Rānēku da dāmā sun wuce kanā cikin tsammāni da tunāni na wōfi da banza. Har zuwa yaushe zā ka mīƙe kwance bisa gadonka? Farka daga barci, ka kuma tāshi maza sabōda rānā tā zō kai-tsaka, wataƙīla kō tā haske ka da kyaukyawan haske.
Yā kai ɗan Adam,
Daga ƙōlin dūtsin tsarkaka, haske yā saukō maka, kuma kan « sināyin » zūciyarka, rūhun annūri yā būsa. Ta haka, ka yi wātsi da yānar tsammāninka na wōfi da banza, kuma ka shigō cikin balbālīna don ka gyāra shirinka na rāyuwa har abada, kuma ka kai matsayin sāduwa da ni. A lōkacin nan, kō mutuwa, kō gajiya, kō kuma matsala, bā zā su isa garēka ba.
Yā kai ɗan Adam
Dawammāta, ita cē halittāta; nā yō ta dalīlinka. Maidā ta alkyabbar ɗākin ibādarka. Kaɗaitakāta, nufīna nē; nā yō ta dōmin ka; maidā ta tufarka don ka zamana wurin bayyanar rāyuwa ta har abada.
Yā kai ɗan Adam,
Martabata ita cē alhērin da na maka, kuma muhimmancīna shaidar rahamātā cē a garēka. Nī kō abun da ya kamāce ni, bā wanda ya isa ya gānē da shi kō ya faɗē shi. A gaskiya nā ɓōye shi cikin rumbun sirrīna, kuma cikin dūkiyar umurnīna, tamkar shaidar alhērina zuwa ga bāyūna da jinƙaina zuwa ga al’ummāta.
Yā ku diyan boyeyyuwar tūshe ta Ubangiji,
Zā a hanā ku ƙaunāta, kuma hankula zā su rūɗe a lōkacin ambatā ta, alhāli ilimi bā ya iya gāne ni, kō zūciya ta kumshē ni.
Yā kai ɗan kyawon halitta,
Don rūhūna da alhurmāta! Don jinƙaina da kyāwōna! Duk abun da na bayyana maka da harshen mulki, kuma duk abun da na rubūta maka da alkalamin ƙudura, sun daidaita da gwalgwadon hankalinka da matsayin iyāwarka, ammā bā daidai da matsayīnā ba, kō kuma da zāƙin muryāta ba.
Yā ku ƴan Adam,
Ba ku san don mi, kū duka muka halicce ku da yumɓu guda ba? Sabōda kar kōwa ya ɗauki kanshi fiye da wani. Ku yi la’akari har kullum da yanda aka halittō ku. Tun da yake, kū duka mun halittō ku daga turɓuwa guda, yā kamāta ku zamana kamar rai ɗaya, kunā tafiya da tāki ɗaya, ku nā abinci da bāki ɗaya, kuma kunā zama cikin ƙasa ɗaya, dōmin cikin zūciyarku, daga duk abubāwan da kuke aikatāwa kō kuke yi, alāmun haɗin kai da tūshen dangana su bayyana. Wannan shī nē galgaɗin da nike muku, yā ku al’ummar haske. Ku ɗauki wannan galgaɗi don ku cirō ƴāƴan tsarkaka daga itāciyar ɗaukaka mai al’ajabi.
Yā ku ƴāƴan rūhu,
Kū nē dūkiyāta, sabōda a garēku nē na binne lu’ulu’un asīrīna da jauharin sanīna. Ku kāre su da munāfikan dake garwaye cikin bāyūna, kuma da kāfiran dake laɓe cikin al’ummāta.
Yā kai dan wanda ya tāshi da kansa a daularsa.
Ka san da cēwa, a garēka, na busa duka turāren tsarkaka, na maka cikakkiyar bayyana ta kalmāta, a garēka, na kammala alhērina, kuma na sō ka da abun da nike sō don kaina. Don haka, ka zamana mai murna da bukātāta, da kuma mai gōdiya a garēni.
Yā kai ɗan adam,
Bisa allon rūhunka, rubūta duka abūbuwan da muka bayyanā maka, da tawadar haske. Idan bā ka iyāwa, ƙēra tawadar da asulin zūciyarka. Idan kuma bā ka iyāwa, tō rubūta da wannan jar tawadar da aka zubda bisan hanyāta. A gaskiya wannan tā fiyē mini da duka sauran ; haskenta yanā tabbata har kullum.
Yā kū māsu ilimin ganēwa da kunnuwan ji !
Gā kira na farko daga wanda Shī nē Abun ƙauna. Yā kē sūdar al’ajabi ! Kar ki nēmi wani wurin zama in bā garkar rūhu ba. Yā kai manzon sulēmānun ƙauna ! Kar ka nēmi wani wurin hūtū in bā kusa da Sābar kaunā ba ; Kuma yā kai tsuntsu mai dawwama har abada, kar ka sauka kō ina in bā bisa tudun aminci ba, nan nē gidanka idan da fiffiken rūhunka, ka tāshi ka nufi daula maras iyāka, kuma idan ka ƙōƙarta ka isa manufarka.
Yā kai ɗan rūhu,
Tsuntsū yanā nēman gidansa, sūda nā nēman kyakkyāwan hure, alhāli waɗannan tsuntsaye, zuƙāccen mutāne, sun gamsu da ƙūra mai wucēwa, sun yi nēsa da shēƙarsu, kuma sun kafa idānuwansu wajen ruwan caɓon sake, sun rasa rahamar Allah. Kaico ! Gā abun māmāki da ban tausayi ! Sabōɗa mōɗa ɗaya tak, sun yi wātsi da tēkun maɗaukakin Sarki, kuma sun yi nīsa da mafi kyaukyāwan tsinkāye.
Yā kai amīnīna,
Kar ka shūka kōmi a cikin garkar zūciyarka in bā furen ƙaunā ba, kar ka dēna rungumar sūdar aminci da sōyayya. Sarkafu da mummunai, kuma ka yi nēsa da kāfirai.
Yā kai ɗan gaskiya,
Inā masōyi zā ya iya zuwa in bā ƙasar masōyiyarsa ba ? Kuma inā mai biɗar da zai cē yā sāmu hūtū alhāli bai sāmu abun da yake biɗā ba ? Wurin masōyin gaske, sāduwa ita cē rāyuwa, kuma rabuwa ita cē mutuwa. Yā yi iyākacin haƙurinsa, kuma zūciyarsa har yanzu ba ta sāmu hūtū ba. Yanā iya sadaukar da dubunnan rāyuka don ya gaggauta gidan masōyiyarsa.
Yā kai ɗan ƙūra
A gaskiya ina shaidā maka cēwa : A cikin duka ƴan adam, mafi sake shī nē wanda yake jāyayya don nēman ya gwada yā fi ɗan uwansa. Ka cē : yā kū ƴan uwāna, ku yi adō da abūbuwan da kuke aikatāwa, ammā bā da maganar fātar bāki ba kawai.
Yā kai ɗan yumɓu
Ka sani fa, zūciyar dake tāre da sauran kwaɗai, har abada, bā zā ta sāmu dāmar shiga daulātā maras iyākā ba, balle ta ji ƙamshin turāren tsarkaka dake saūkōwa daga fādāta mafi tsarkaka.
Yā kai ɗan sōyayya,
Tāki ɗaya tak ya rabā ka da ɗaukaka, kuma da itāciyar ƙauna ta samāniya. Ƙōƙarta ka yi tāki na farkō, kuma a na biyu, ka nufi daula maras ƙārēwa, kuma ka shiga zauren dake kafe har abada. A nan, sai ka saurari abun da alƙalamin ɗaukaka ya bayyana.
Yā kai ɗan ɗaukaka,
I hanzari bisa hanyar tsarkaka, kuma sāmu shiga samāniyar sāduwa da ni. Wanke zūciyarka da hasken rūhū, kuma zābura zuwa fādar Mai sama.
Yā kē inuwa mai gushēwa,
Ƙētara ƙasƙantaccen matsayin shakka, kuma haye ƙōlin tabbata mafi ɗaukaka. Būɗe idon gaskiya dan ki dūbi shāwā bā tāre da wata kāriya ba, kuma ki shēdā cēwa : Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Wanda Shī nē mahīhīcin mahalitta.
Yā kai ɗan buƙāta,
Saurāri wannan da kyau : har abada idō bā zā ya ga kyawō maras iyāka ba, kuma matacciyar zūciya bā ta ɗanɗana hūre ba, sai mai yaushi, sabōda kōwa yanā biɗar daidai da shi, kuma yanā jin dāɗin zama da makamantansa.
Yā kai ɗan ƙūra,
Maida kanka makāho don ka sāmu hālin ganin shāwāta : līƙe kunnuwanka don ka ji dāɗin wāƙar muryāta ; i wātsi da duk wani ilimi don mu raba sanīna ; kuma ka rabu da duk wata dukiyar dūniya, don ka dāce da sāmun daɗaɗɗen rabo daga cikin kōgin arzikīna maras ƙārēwa. Abun nufi shī nē : ka makabta ga kōmi bāya ga shāwāta ; ka kurumta ga kōmi bāya ga maganāta ; ka yi wātsi da duk wani ilimi banda sanīna, dōmin, idan kanā gani warai, kanā da tsarkakakkiyar zūciya, da kuma kunnuwa māsu ji garau, kā sāmu shiga daulāta mai tsarki.
Yā kai dan adam mai lūra biyu,
Rufe ijiya ɗaya, kuma ka buɗe gudar. Rufe ta farkon ga dūniya da duk abun da ta ƙumsa, kuma ka buɗe na biyun don ganin tsarkakakken kyāwon wanda shī nē Abun ƙauna.
Yā ku ƴāƴāna,
Inā tsōron kar rishin kūkan kurciyar samāniya ya sā ku sāke fāɗāwa cikin zurfin duhun ɓata, kuma a kan ba ku sāmu ganin kyāwon hure ba, ku kōma cikin ruwa da caɓo.
Yā kū aminnaina,
Kar ku yi wātsi da kyāwō maras iyāka sabōda shāwā mai wucēwa, kuma kar ku rungumi dūniyar nan mai ƙārēwa.
Yā kai ɗan rūhu,
Wata rānā nā zuwa, wadda sūdar tsarkaka zā ta daina bayyana tūshen gaibu, a lōkacin nan kū duka ba zā ku ji wāƙā daga samāniya ba, kuma bayyāni zai daina saukōwa daga samāniya.
Yā kai irin sakaci,
Dubunnan bayyānai zuwa ga Ubangiji sun kasance cikin jawābi guda ɗaya, kuma dubunnan gaibu sun bayyana cikin launin wāƙā guda ɗaya. Ammā inā ! Bābu kunnuwa māsu ji kō zūkāce māsu fahinta.
Yā kū abōkaina,
An būɗe ƙōfōfin hanya maras iyāka, kuma gā shi mabartar Wanda Shī nē abun ƙauna tā yi adō da jinin masōya ; ammā duk da haka, mutāne in bā ɗaiɗaya ba, sun nīsanta da wannan birnin samāniya, kuma cikin ƴan kaɗan kin mā, ɗaiɗaya nē māsu farar zūciya da nufi tsarkakakke.
Yā kū dake cikin muhimmiyar aljanna,
Ku gaya mā ƴāƴan haƙīƙa da cēwa, a cikin daular tsarkaka dake kusa da aljannar samāniya, wata sābuwar garkā, inda bāƙin Mabuwāyi, da rāyayyun aljanna na har abada suke yāwatāwa, tā bayyana. Ku ƙōƙarta tun da wuri ku sāmu shiga, don ku gāne ma’anar ƙauna a cikin hure, kuma a cikin ƴāƴan ku bincikō asīrin basīrar dake wurin Allāhu. Kwanciyar hankali nā tāre da wanɗanda suka shiga, kuma suka sāmu zama cikin wannan daular.
Yā kū amminnaina,
Kun mance da wannan babbar sāhiya mai martaba, lōkacin da kuka tāru duk a gabāna cikin waɗannan wurāre tsarkakakku māsu albarka, ƙalƙashin inuwar itāciyar nan mai rāyarwa dake shūke cikin aljanna? Kunā saurārē nā cikin tsōrō a lōkacin da nike bayyana muku ayōyin nan mafi tsarki: Yā kū aminnaina! Kar ku fi son bin nufinku da nāwa. Kar ku yi ƙaunar abun da nī bā nā ƙauna a garēku, kuma kar ku isō wajēna da zukātan da bā su da rai, waɗanda haɗama da son abun dūniya suka ɓātā. In dā zā ku iya tsarkake rāyukanku, dā kun sāmu hālin tunāwa a yanzun nan, da wannan wuri da abun da yake kēwaye da shi, kuma, dā gaskiyar kalmōmīna tanā fitōwa kōwannanku a fīlī.
Cikin ayōyi māsu tsarki, a lāyi na takwas, bisa allō na biyar, dake aljanna, yā bayyanā cēwa:
Yā kū wanɗanda kuke kwance kamar matattu bisa shinfiɗar sakaci,
Shēkara da shēkaru sun wuce, gā shi rāyukanku sunā nufa wajen ƙarshensu, ammā har yanzu bābu numfāshi mai tsarki da ya isō fādarmu mafi tsarki. Kō da yake kun nitse cikin zurfin tēkun taurin kai, ai kuwa lēɓunanku nā ambatar addīnnin Allah wanda yake shī nē na gaskiya. Wanda nike ƙiyāma, kun gwada masa ƙauna, maƙiyīna shī nē kuka maida amīninku. Ammā duk da haka, ku nā tāmaƙa ku nā tāka ƙasāta, ba ku san da tā gaji da ku ba, har mā duk abun da ta ƙunsa nā gōce maku. Dā dai ku nā iya būɗe idānuwanku, dā kun gwammace dubun azāba māsu tsanani, fiye da wannan jin-dāɗi, kuma dā mutuwa mā tā fiye muku da wannan rāyuwar.
Yā kai suffar ƙūra mai mōtsi !
Inā nēman bayyāni da kai, ammā kā ƙi amince mani. Takōbin tāwāyenka yā sāre itāciyar tsamāninka. Kullum inā kusa da kai, ammā kai, har kullum kanā nīsa da ni. Nā zāɓar maka ɗaukaka maras iyāka, ammā kai, kā fi son ƙasƙanci maras iyāka. Tun da sauran lōkaci, dāwō don kar sa’arka ta kubce maka.
Yā kai ɗan buƙāta,
Shēkara da shēkaru masani da mai basīra sun nēmi isā fādar maɗaukakin Sarki, ba su dāce ba, duka rāyuwarsu, sun yi ɓidā ammā ba su sāmu sāduwa da fuskarsa ba. Kai kuma, bā tāre da kā yi wata wahala ba, buƙātarka ta biya, kuma ba ka nēmā ba kā sāmu abun da kake biɗa. Duk da haka, har yanzu, kā tsaya cikin yānar isarka har mā idānuwanka ba su sāmu ganin kyāwon Wanda Shī nē Abun ƙauna ba, kuma hannunka bai sāmu dafa harshen rīgarsa ba. Yā kū dake da idānuwan gani, ku dūbā ku yi māmāki.
Yā kū dake zaune cikin birnin ƙauna,
Gūguwōyi māsu ƙarfin gaske sun kēwaye makāmashi na har abada, kuma baƙar ƙūrā tā ɓōye kyāwon sarmayin samāniya. Al’ummar danniya tā murkushe sarkin sarākunan ƙauna, kuma sūdar tsarkaka tanā kāme tsakanin faratan mūjiyōyi. Ƴan cikin zauren ɗaukaka da jama’ar samāniya nā ƙārā da kuka, a lōkacin da kuke nan zaune cikin daularku ta rashin kulāwa, alhāli kuwa, ku nā sā kanku cikin aminnaina na gaske. Aikin banza nē tsammānin nan nāku.
Yā kū marassa hankali da ake ɗauka a kan māsu basīra,
Ta ƙāƙā kuke da alāmun makiyāyā, alhāli kuwa kun zamana kūrāye dake kaiwa garkēna hari? Ku nā kamā da tarmāmuwar nan mai ɓullōwa gabannin asubba dake kamar haske da walkiya, ammā sai ta nā ɓatar da māsu tafiya zuwa birnīnā, kuma ta nā sā su hanyōyin ɓata.
Yā kū māsu kamar nagari alhāli daga zūci kū lālātattu nē,
Ku nā kamā da ruwa nagari, ammā māsu ɗāci, daga haka garai kamar ƙanƙara, ammā waɗanda bāyan bahasin Ma’aikin Ubangiji, kō ɗigō ɗaya bā yā karɓuwa. Haƙīƙa, hasken rānā nā haske ƙūra da madūbi daidai wa daida, ammā hasken da kōwannensu yakē mayarwā sun bambanta kamar na tarmāmuwa da na ƙāsa. Mai zan cē ! Wannan bambancin bā shi da iyāka.
Yā kai abōki daga bāki,
Ka yi tunāni kaɗan. Inā ka taba jin inda zūciya guda ta ƙunshi masōyi da maƙīyi ? Kōre bāƙō don amīnī ya sāmu shiga gidansa.
Yā kai ɗan ƙūra,
Duk abūbuwan dake sama da ƙasa nā yi su dōmin kai, ammā banda zūciyar ɗan adam da na maida mazaunin kyāwōna da ɗaukakata. Ammā gāshi kā sā wani da bā nī ba a cikin gidāna da mabartātā. A lōkacin da wahayin tsarkakāta ya sō shiga gidansa, sai ya iske kā sauke wani bākō da ba shī ba ; da yake yā rasa masaukinsa, sai ya gaggauta wajen zauren Wanda Shī nē Abun ƙauna. Duk da haka, nā rufa maka asīri kuma ban sō kunyatā ka ba.
Yā kai irin buƙāta
Sau da yawa nā yi assubanci gidanka tun daga daulōli maras iyāka, sai in tardā ka kwance a bisa gadon hūtū, ka nā kulāwa da wanɗanda bā nī ba. Sai kamar walƙiyar rūhū, in kōma wajen daulōlin daukakar samāniya daga wannan wurin fakēwāta dae bisa, ban shaidāwa rundunōnin tsarkaka ba abun da ya wakāna.
Yā kai ɗan alhēri,
Daga cikin hamādar rishin rāyuwa, da yumɓun ikōna, na halitto ka, kuma na damƙa rēnonka ga kōwace ƙwāyar halitta, kuma ga tūshen duka abūbuwan dake halicce. Don haka, tun kāfin ka fitō daga ma’aifa, na kēɓē maka mashāyar nōnō guda biyu tsabtatattu: idānuwa da zā su riƙa kiyāye ka, kuma da zūciyōyi da zā su ƙaunar ka. A cikin kyautatāwāta, kuma ƙalƙashin inuwar rahamāta, na rāyā ka, hallau da tūshen alhurmāta da alhērina, na kiyāye ka. Abun nufīnā ga duka wannan shī nē: in sā ka shigā cikin daulāta maras iyāka, kuma ka dāce mai ƙarbar baiwāta dake ɓōye. Ammā sai ba ka dāmu da yin haka ba, har mā da girmanka, sai ka manta da duk waɗannan alhēri da na maka, ka bi tsammāninka na wōfi da ya kai ka inda ka shagala gabāɗaya, kuma bāyan kā jūyāwa ƙōfōfin amīnī bāyā, ka ƙaura gidan maƙīyīna.
Yā kai bāwan dūniya,
Sau dayawa, bazarar amincīna tā yi maka assubanci, ammā sai ta tarda ka nā kwānā mai zurfi, bisa shimfidar sakaci. Sai ta kōma inda ta fitō ta nā kūka da ganin hālin da kake ciki.
Yā kai ɗan ƙasā,
Idan nī kake buƙāta, kar ka nēmi wani bā nī ba; kuma idan ka nā buƙātar kallon kyāwōna, ka rufe idānuwanka ga dūniya da duka abun da ta ƙunsa. Don ka san da cēwa, kamar yanda wutā da ruwa bā su zama wuri ɗaya, haka yardāta da yardar wani da bā nī ba, bā su iya maƙwabtaka cikin zūciya guda.
Yā kai baƙon da aka amince da kai,
Hannun ikōna yā hūra wutar zūciyarka, kar ka kashe ta da iskar son kai da haɗama. Kar ka manta da cēwa, tunāwa da ni shī nē warkēwa daga duka matsalōlinka. Maida ƙaunāta dūkiya a garēka, kuma ka yi tattalin ta kamar idānuwanka, har mā kamar ranka.
Yā kai ɗan uwāna,
Saurāri magana mai zāƙin zuma dake fitōwa daga harshēna, kuma ka shā a ƙōramar tsarkaka dake ɓullōwa daga lēɓunāna māsu fiddō ruwa mai zaƙin zuma. Shūka ƙwāyōyin basīrāta cikin tsabtacciyar fadamar zūciyarka, kuma bā su ruwan haƙīƙan don shūkōkin sanīna da basīrata su fitō tsanwa shar cikin birnin zūciyarka mai tsarki.
Yā kū mazaunan aljannāta,
Da hannuwāna māsu ni’ima, nā shūka ƙaramar itāciyar ƙaunarku da amincinku cikin balbālin aljanna mai tsarki, nā bā ta ruwa mai yawa na rahamāta mai taushi. Yanzu da zā ta fāra ƴāƴā, sai ku ƙōƙarta ku kāre ta, don kar azābar bēgen dūniya da haɗama ta māmaye ta.
Yā kū aminnaina
Cikin zūciyarku, ku kashe fitilar kuskure don ku kunna makāmashin haniyar Ubangiji maras ƙārēwa. Sabōda nan gaba, a fādar wanda shī nē abun yabo, māsu binciken ayyukan ƴan adam bā zā su ƙāra yarda da kōmi ba, sai kawai hālin ibāda da aikin tsarkaka.
Yā kai ɗan ƙura,
Mutun mai basīra shī nē wanda bā ya magana sai ana sauraran sa, kamar yanda ba a mika mōɗa sai ga mai jin ƙishurwa, kō kuma kamar yanda masōyi bā ya fiddō ƙaunar dake cikin zurfin zūciyarsa sai yā sādu da kyāwon masōyiyarsa. Kēnan, ku shūka ƙwāyōyin basīra da hikima cikin gōnar zūciya mai tsarki, kuma ku bar su a nan ɓōye har lōkacin da huren basīrar Allāhu ya tōhō daga cikin wannan zūciyar, bā daga cikin caɓo da lākā ba.
Yā kai bāwāna,
Kar ka yi wātsi da daula maras iyāka sabōda abu mai ƙārēwa, kuma kar ka yi jīfa da martabar samāniya don nēman biyan buƙātar dūniya. Wannan shī nē gulbin rāyuwa maras iyāka da ya ɓullo daga marmaron alƙalamin Rahimun. Murna ta tabbata ga waɗanda suka shā a wannan gulbi.
Yā kai ɗan rūhu,
Rūshe akurkin da kake ciki, kuma kamar tsuntsun ƙauna, ka hira wajen samāniyar tsarkaka. Manta da kanka, kuma ɗauke da rūhun jinƙai zauna daular tsarkaka ta Ubangiji.
Yai kai irin ƙūra,
Kar ka dangana da jin-dāɗin rānā ɗaya mai gujēwa, kuma kar ka hana kanka hūtū na har abada. Kar ka rungumi iskar dūniya mai wucēwa, kambacin lambun jin-dāɗin rāyuwa maras ƙārēwa. Fita daga kurkukun da kake ciki, ka hira zuwa fadamar samāniya mai ɗaukaka, kuma daga akurkinka mai macēwa tāshi zuwa aljanna maras iyāka.
Yā kai bāwāna,
Kuɓuta daga sarƙōƙin wannan dūniyar, kuma ka tsirar da ranka daga kurkukun son-kai. Kāma sa’arka tun ta nā gabanka, tunda dai bā zā ta ƙāra dāwōwa garēka ba.
Yā kai ɗan baiwāta,
In dā kanā iya ganin daular rāyuwa har abada, ai dā kā zābura kā bar wannan dūniya mai wucēwa. Ammā, ɓōye maka wancen da kuma bayyanā maka wannan, yanā cikin asīrin da ya gāgara fahinta sai ga mai tsarkakakkiyar zūciya.
Yai kai bāwāna,
Tsarkake zūciyarka daga duk wata mugunta, kuma manta da duk wata buƙāta ka shiga cikin balbālin Ubangiji Allah mafi tsarki.
Yā kū aminnaina,
Ku zāgaya bisa hanyōyin jin-dāɗin Amīni, kuma ku san da cēwa, jin-dāɗinsa shī nē na halittunsa. Abun nufi shī ne: bā wanda yake da hālin shiga gidan amīninsa, kō kuma ya taɓa dūkiyarsa bā tāre da izininsa ba, haka kuma, bai kamāta ba ka sō buƙātunka hiye da nāsa, kuma kō ta ƙāƙā, kar ka nēmi ƙāruwa a bisansa. Ku yi tunāni a kan haka, yā kū māsu hankalin gānēwa.
Yā kai abōkin gadon mulkīna
Kar ka saurāri laifi, kuma kar ka dūbi laifi; kar ka ƙasƙanta kanka, kuma kar ka yarda a ji jāje kō kūka a garēka. Kar ka yi da wani dōmin kar ka ji an yi da kai, kar ka tsananta laifukan waɗansu dōmin kar nāka laifukan su tsananta; kar ka nēmi kunyata kōwa don kar tāka kunyar ta fitō hīlī. Cikin rāyuwarka ta dūniya mai sauƙin wucēwa, tsarkake zūciyarka, rūhunka ya zama tsabtacce, kuma nuhinka ya ƙunshi alhēri, hālinka gabāɗaya ya tsarkaka. A lōkacin nan, cikin murna da ƴanci, ka nā iya huta daga salkarka mai macēwa ka kōma cikin aljanna, kuma ka zauna har abada cikin daular Madawwami.
Kaico, kaico! yā kū waɗanda kuka sarƙafa da buƙātun dūniya
Wuluk kamar walƙiya kuka wuce kusan wanda shī nē abun ƙauna kuma zukācenku suka rungumi ra’ayōyin shēɗan. kunā durƙusāwa gaban tsammāninku na wōfi da banza da kuke kira gaskiya. kunā jūya fuskarku wajen ƙaya da kuka bā ta sūnan hure. Bābu numfāshi mai tsarkaka da ya fitō daga fadamōmin zukātanku. Kun yi wātsi da galgaɗin wanda shī nē abun ƙauna, kuma kun ƙanƙare su sam-sam daga bisa allon zukātanku; kuma kamar nāmōmin dāji, ku nā zirgā-zirgā, kuma ku nā rāyuwa cikin garāken murādi da kwaɗan dūniya.
Yā kū abōkan tafiyāta,
Don mi kuka yi sake da yabon Wanda Shī nē Abun ƙauna, kuma don mi kuka tsaya nēsa da daularsa? Wadda ita cē iyākar kyāwō ta nā cikin zaure mafi kwatamci, zaune a bisa gadon ikon ɗaukaka, alhāli ku nā jāye–jāyen wōfi. Gā ƙamshin turāren ɗaukaka, da sanyin alhurma sun bazu. Alhāli ku nā cikin mummūnar matsala nēsa da waɗannan karāmōmi. Allah ya wadan ku, kū da māsu bin umurniku.
Yā kū ƴāƴan buƙāta,
Ku fitar da tufāfin ƙarya, kuma ku tūɓe rigar girman kai.
A cikin lāyi na ukku na lāyuka mafi tsarki, a bisa allon jan yāƙūtu, alƙalamin wanda shī nē ya fi ƙarfin a gan shi yā rubutā cēwa:
Yā kū ƴan uwāna,
Ku kasance māsu lāfiya da rangwame da jūna, kuma kada ku sarƙafa da abun dūniya. Kada ku gwadi girman kai cikin sāmu, kō kuma ku ji kunya cikin rashi. Nā ranste da kyāwōna! Nā halittō kōmi daga ƙūra, kuma cikin ƙūra zan mayar da kōmi.
Yā kū ƴāƴan ƙūra
Ku sanar da attājiri darūrōrin da matalauci kē ciki kōwane dare, don tsōron kada sakacinsu ya sā su hanyar hallaka kuma ya hanā su isā ga itāciyar arziki. Yin kyauta da gwadin yin karāma sunā biyu daga cikin kirārīna: murna ta tabbata ga wanda ya yi adō da nagartattun halāyēna.
Yā kū ainafin haɗama
Ku rabu da duk wani kwaɗai kuma ku iya dangana da matsayinku; tunda dai makwaɗaici bā ya tāre da sāmū, ammā kuwa mahaƙurci har kullum yanā tāre da ƙauna, kuma shī nē abun yabo.
Yā kai ɗan baiwāta,
Kada ka dāmu don kanā cikin talauci, kuma kada ka yi fankama don kanā da arziki. Ka san da cēwa: bāyan talauci sai arziki, kuma bayan arziki sai talauci. Ammā duk da haka, rashin kōmi bāya ga sanin allah shī nē baiwa mafi ban māmāki; kada ka rēna wannan daraja, sabōda a ƙarshe wannan nā arzutā ka gaban Ubangiji; a lōkacin nan nē zā ka gāne da ma’anar wannan Magana mai cēwa: “A gaskiya kū matalauta nē”, kuma wannan bayyāni mai tsarki “Allah shī nē mai kōwa mai kōmi” zā ya bayyana, kamar sāhiyar ainafi, dake wātsa cikakken haskenta cikin zūciyar masōyi, kuma a lōkacin nan zā ka ga kanka cikin lumāna bisa gadon arziki.
Yā kū ƴāƴan sakaci da haɗama,
Kun bar maƙiyīna yā shiga gidāna, kuma kun kōre masōyina daga nan, alhāli kun būɗe zukātanku ga sōyayyar wani da bā nī ba. Ku saurāri abun da amīni ya faɗa, kuma ku nufi zuwa aljannarsa. Amīnnan dūniya, cikin biɗar buƙātarsu, sunā nūna kamar sunā ƙaunar jūna, alhāli kuwa shi Amīni yā fi son ku, kuma yanā cikin son ku don kanku: a gaskiya, yā yi jimirin wahalōli māsu ɗunbun yawa dōmin ya sā ku hanya. Kada ku ci amānar irin wannan Amīni, a’a, ku gaggauta dai zuwa wajensa. Wannan shī nē hasken rānar gaskiya da aminci da ta ɓullō daga alƙalamin Ubangijin duka sūnāye, ku būɗe kunnuwanku don ku ji bayyānin Ubangiji Allah, mai cēto cikin hallaka, wandan yake rāyuwa cikin ikonsa.
Yā kū māsu tāmaƙa da dūkiya mai ƙārēwa,
Ku san da cēwa: a gaskiya, dūkiya shingē cē mai fāɗi tsakānin mai nēmā da abunda yake nēmā, tsakānin masōyi da abun ƙaunarsa. Attājirai, ban da ƴan kaɗannan, bā zā su sāmu shiga ba cikin fādarsa kō ta ƙāƙā, kuma bā zā su sāmu shiga ba cikin birnin jin-ɗādi da dangana ba. Sabōda haka, murna ta tabbata ga attājirin da arzikinsa bai kauce shi daga daula maras iyāka ba, kuma bai hana shi shiga fādā maras ƙārēwa ba. Nā rantse da Babban Sūna! Martabar wannan mutunan zā ta haske al’ummar samāniya kamar yadda rānā take haske al’ummar dūniya.
Yā kū attājiran dūniyar nan,
Matalauta ajjiyāta cē a gāreku. Ku kula da wannan ajjiya, kuma kada hankalinku ya ɗauku ga jin-dāɗin rāyuwaku kaɗai.
Yā kai ɗan annashuwa,
Tsarkake kanka daga dauɗar dūkiya, kuma a kan hankali kwance, ka nufi wajen daular talauci, dan ka sāmu shan ruwan zumuwar rāyuwa ta har abada daga marmaron rishin sarƙafa.
Yā kai ɗāna
Zamā tāre da marassa imāni yanā ƙāra ɓācin rai, ammā zumunci da adalai yanā wanke tsātsar zūciya. Duk mai nēman sāduwa da Ubangiji Allah, tō ya nēmi zama cikin aminnansa ; kuma duk mai nēman jin bayyānin Ubangaji Allah, tō ya saurāri bayyānin zāɓaɓɓun bāyunsa.
Yā kai ɗan ƙūra,
Kashēdi ! kiyāye kanka da tafiya da maras imāni, kuma kada ka nēmi yin ƙungiya da shi, sabōda irin wannan dangantaka nā maida hasken zūciya kamar wutar jahannama.
Yā kai ɗan baiwāta,
Idan kanā buƙātar alhumar Rūhu Mai tsarki ta tabatta a garēka, tō ka nēmi aminci da ādali, sabōda shi ya sāmu shan ruwan rāyarwa na har abada, kuma kamar farar sāhiya, yanā rāya zukātan matattu, kuma yanā haskake su.
Yā kū māsu sakaci
Kar ku yi zaton kō ba Mu san asiran dake cikin zukāce ba ; sai mā ku tabbata da ashe, sunā rubuce warai, kuma gwaro-gwaro a gaban Fādar Mai tsarki.
Yā kū aminnaina,
A gaskiya, ku san da cēwa, duk abūbuwan da kuka ƙunshe cikin zukātanku, bayyanannu nē a gāreMu kamar hasken rānā. Mun bar su a ɓōye bā don halinku ba, kawai don alfurmarmu da yalwarmu.
Yā kai ɗan adam,
Bisa al’ummar dūniya, nā yayyafa ɗigon rāɓar tēkun rahamāta maras iyāka, ammā ban ga wanda ya yi amfani da shi ba; alhāli, dukan mutāne sun bar ruwan samāniya mai haɗa kai, sun jūya hankalinsu wajan ruwan dauɗa, kuma sun yi wātsi da ƙwaryar ruwan shāwā maras iyāka, sun shā cikin mōɗar ruwa mai kashēwa, Allah wadan wannan buƙāta tāsu.
Yā kai ɗan ƙūra,
Kada ka yi wātsi da ruwa mafi kwatanci da Wanda Shī nē Abun ƙauna Madawwami yake mīƙā maka, kuma kada ka jūya fuskarka wajen caɓo mai guba. Karɓi ƙwaryar rāyuwa maras ƙārēwa daga hannun Wanda Ubangiji ya zāɓā, don duk basīra ta tabbata a garēka, kuma dan ka iya jin muryar dake kirā daga fādar Wanda yake ɓōye. Ka ɗaga murya cēwa: yā kū māsu gajēren tsinkāye, yāyā kuke wātsi da ruwāna mai tsarkaka rāyuwa har abada, sabōda ruwa mai ƙafēwa?
Yā kū al’umman dūniya,
Ku san da cēwa, wata allōba da bā ku tsammāni tanā biye da ku, kuma azāba mai tsanani nā jiran ku. Kar ku yi tammaha cēwa: duk abūbuwan da ku ka aikata nā manta da su. Nā rantse da kyawōna, alƙalamīna yā bugā su gwarō-gwarō bisa allunan dūtsi.
Yā kū azzāluman sarākunan dūniya,
Ku dēna zālumci, sabōda nā ɗauki alkawarin bā zā ni gāfartāwa ɗan adam ba kōwane hā’incin da zai aikata. Wannan alkawarīnā nē da na tsaida a rāɗin kaina, kuma na rubūtā shi bisa ādanannan allō mai hātimin ɗaukakāta.
Yā kū ƴan dandi,
Rangwamēna a garāku yā bā ku dāmā, kuma haƙurīna yā sā kunā sakaci har ku ka kai hawa bisa ingarmin dōkin annashuwa, kuka nufi da shi bisa hanyōyin hallaka māsu kai ku ga ɓata. Kun ɗauke Ni masakaci nē, kō kuma kunā ganin ina cikin jahilci nē?
Yā kū māsu hijira,
An yi harshe don ya ambacē Ni, kar ku ɓātā shi da dauɗar ƙaskanta wani. Idan wutar son-kai ta fāra cin ku, ku yi tunāni da laifukanku ammā bā na halittūna ba, alhāli, kōwa yā fi sanin kansa fiye da yanda ya san waɗansu.
Yā kū ƴāƴan tsammāni,
Ku san haƙīƙan da cēwa, a lōkacin da farar assuba take saukōwa daga samāniyar tsarkaka ta har abada, asīran shēɗanci da duk wasu miyāgun ayyuka da aka aikata cikin duhu, zā su bayyana a fīlī gaban duka al’ummar dūniya.
Yā kē mūguwar ciyāwa da kika tsiro daga cikin ƙūra,
Yāyā aka yi ba ki shāfi tufāfinki ba da farko da ƙazamman hannuwan nan nāki, kuma ta ƙāƙā zā ki nēmi sāduwa da ni, kuma ki shiga cikin daulāta mai tsarki, alhāli zūciyarki tā dāmu cikin marmari da son abun dūniya ? Kaico, kun yi nīsa, kun yi nīsa ƙwarai da abun da kuke biɗa !
Yā kū ƴan Adam,
Kalmōmi māsu imāni, da kyaukkyāwan ayyuka māsu tsarki sunā nufa wajen samāniyar ɗaukaka. Ku yi yanda zā ku karkaɗe ƙurar son-kai da munāfuci daga ayyukanku don ku sāmu rangwame a fādar ɗaukaka ; ku san da cēwa nan gaba, māsu buncika ayyukan yan adam, bā zā su ƙāra yarda da kōmi ba da ya isa fadar Wanda Shī nē Abun yabo, sai ibāda ta gaske da ayyuka māsu muhimmin kyau, wannan ita cē rānar basīra da asīrin Ubangiji, da ta haska a samāniyar nufin Allah. Albarka ta tabbata ga waɗanda suka jūya fuskarsu wanjensa.
Yā kai ɗan rāgaita
Daular bayyana tanā da dāɗi idan ka isa garēta ; wurin rāyuwa na har abada yanā da ɗaukaka, idan ka ƙētara dūniyar mutuwa ; wuridi mai zurfi cikin tsarkaka yanā da dāɗi idan ka shā ruwan rūhun mōɗar da Sarmayin ilāhi ya mīƙa maka. Idan ka sāmu wannan matsayin, tō zā ka rabu da hallaka da kuma mutuwa, da tsanantacciyar wahala, kuma da ɗaukan zunubi.
Yā kū aminnaina
Ku tuna da wannan alkawari da kuka ɗauka tāre da Ni bisa tudun « Ɗāran », wanda yake cikin tsarkakken fīlin « Zāman ». Mataimakin samāniya da al’ummar birnin rāyuwa har abada sūnē shaidūna; ammā gā shi yau, ban ga wanda ya riƙe wannan alkawari ba. Bā shakka girman-kai da rishin biyayya sūnē suka shāfe wannan alkawari daga zukātanku har ya zamanto bābu kō ƙurarsa. Duk da haka, cikin nā san da wannan, na dākata kuma ban bayyanā shi ba.
Yā kai bāwāna,
Kana kama da takōbi mai kaifi dake ɓōye cikin baƙin kube, kuma wanda maƙērinsa bai san darajarsa ba. Kēnan ka fito daga cikin rāmin son-kai da haɗama, dōmin darajarka ta bayyana, kuma duk dūniya ta shaida da ita.
Yā kai amīnīna
Kai nē rānar samāniyar tsarkakāta, kada ka yarda dauɗar dūniya ta ɓadda haskenka. Tsāga yānar sakaci dōmin ka ɓullō warai daga cikin gizāgizai, kuma ka yi mā kōmi adō da rīgar rāyuwa.
Yā kū ƴāƴan fankama,
Kun yi wātsi da daulāta maras iyāka sabōda ƴanci mai wucēwa. Kun yi adō da ƙyalƙyalin dūniya da kuka maida abun gūrinku. Nā rantse da kyawōna cēwa: sai nā tattarā ku gabāɗayanku ƙarƙashin yānar ƙūra mai launi ɗaya tak, kuma in fiddāwa kōwannanku ire-iren launin da kuke tāre da shi, banda waɗanda suka zāɓi nāwa launin, launin dake tsarkake da duk wani launi.
Yā kū ƴāƴan sakaci,
Kar ku yarda ku zauna cikin wadāta mai wucēwa, kuma kada ku yi murma da haka. Kunā kamā da wannan tsuntsun maras tsinkāye da yake rēra wāƙā cikin yardā a bisa rēshen itāciya, har lōkacin da mai kāmun tsuntsaye ya hallakā shi ya mayar da shi ga ƙūra; a lōkacin nan sai duk waɗansu salon wāƙā, kamannu, da launi su ɓace gabāɗayansu bā tāre da sun bar shaida ba. Don haka, ku yi hankali da kanku, yā kū bāyun murādi.
Yā kai ɗan baiwāta,
Har zuwa lōkacin nan, umurnai sun kasance kullum faɗar fātar bāki cē, ammā yanzu, aikatāwa ita cē mai tsayar da umurni. Yā kamāta kōwa ya maida niyya wajen aikata abun kirki, kuma mai tsarki, sabōda ita magana ta kōwa cē, alhāli irin waɗannan ayyuka sai aminnanmu kawai. Ku ƙōƙarta da zūciya ɗaya, kuma tsakāninku da Allah, ku bambanta, ku yi sūnā cikin ayyukanku. Wannan ita cē shāwarar da Muke bā ku a rubuce cikin wannan tsarkakekken allō mai haske.
Yā kai ɗan ādalci,
Cikin dare, kyāwon wanda shī nē mai rāyuwa har abada, yā saukō daga tudun aminci wanda yake tsanwa shar, yā isa «Sadaratu’l Muntaha », kuma yā yi ta zubda hawāye har ya kai inda Majalisar ƙōli da al’umman samāniya suka fāra gunāguni gaban koke-kokenshi. A lōkacin da aka tambaye shi dalilin kōke-kōken da gunāgunin da yake yi, sai ya ce: Kamar yanda aka umurcē ni, inā cikin jira, a bisa tudun aminci, sai ban ji ƙanshin turāren amincin mutānen dūniya ba. Da aka umurcē ni da dāwōwa, ina dūbāwa sai na tsinkāyi, waɗansu sūdōdin tsarkaka sunā kāme sunā shan bakar wuyā cikin farātan karnukan dūniya. A lōkacin nan, sai malā’ikar samāniya ta hudda lulluɓinta, ta zāburo daga mazauninta ta tambayi sūnāyensu; a lōkacin nan, an bā ta duka sūnāyen banda guda daya tak. Da ta matsa, sai aka bayyana baƙi na farko; daga jin haka, sai al’ummar dake mazaunin samāniya suka zāburo da gudu daga gidājensu na ɗaukaka. Da aka faɗi baƙi na biyu, duk gabāɗayansu sai suka zuɓe cikin ƙūra. A lōkacin nan, sai aka ji wata murya tā fitō daga ƙuryar ɗākin ibāda tanā cēwa: « har zuwa nan, kuma kar a wuce nan ». A gaskiya, munā shaidar abun da suka aikata, kuma da abun da suke cikin aikatāwa.
Yā kai ɗan baiwāta,
Shā ruwan ƙōrāmar gaibun Madawwami dake fitōwa daga lēɓunan Rahimun, kuma dūbi ɗaukakar rānar basīra, bā tāre da wata yānā ba, daga marmaron bayyānin Allah. Shūka ƙwāyōyin basīrāta cikin gōnar zūciya mai tsarki, kuma ka bā su ruwan tabbata, dōmin tōhon sani da basīra su tsirō tsanwā shar daga tsarkakakken birnin zūciya.
Yā kai ɗan buƙāta,
Har zuwa yaushe zā ka riƙa hirā cikin jahōhin bukāta? Nā bā ka fikāfikai sabōda ka sāmu dāmar hirā wajen daulōlin tsarkaka, ammā bā don ka nufi wajen jahōhin zatō da tsammāni na shēɗan ba. Nā bā ka matsēfi don ka gyāra mani baƙar sumāta, ammā ba don ka karce mani maƙōshi ba.
Yā ku bayūna,
Kū, itācen lambūna nē; yā kamāta ku bāda ƴāƴā na ƙwarai, kuma kyaukyāwa, dōmin ku ci mōriyarsu, kū da sauran jama’a. Don haka ya cancanta kōwa ya kāma aiki kō wata sāna’a, dōmin wannan ita cē hanyar arziki, yā kū mutāne māsu lūra. Ku san da cēwa, hanyōyin ɗā’a suke bāda sakāmakon alhēri, kuma albarkar Ubangiji zā ta wadācē ku. Itācen da bā su bāda ƴāƴā, har kullum bā su da wani amfani banda hūra wuta.
Yā kai bāwāna
Maƙasƙantan mutāne sū nē wanɗanda ba su amfana kōmi ba a nan dūniya. Waɗannan su nā kamā da matattu, har mā in cē gāra matattun mā ga fuskar Ubangiji da waɗannan rāyuka māsu ragwanci da rishin daraja.
Yā kai bāwāna,
Mutāne mafi daraja sū nē māsu nēman abincinsu cikin albarkar aikinsu, kuma da ƙaunar Allah Ubangijin duka dūniyōyi, su nā kashe dūkiyarsu don rāyuwarsu da ta kamanninsu.
Cikin alhurma da yalwar Ubangiji Allah, wannan kyaukyāwar Amaryar rūhu, wadda har yau take ɓōye a lulluɓe cikin mayāfin bayyāni, yanzu gā ta, tā fitō fīlī cikin haske da kyāwon masōyi yake wātsōwa. Nā shaida yā kū aminnaina da cēwa, alhērin bā shi da iyāka, tambaya ta sāmu cikakkiyar amsa, hujja ta bayyana, kuma tā tabbata a garēku.
Yanzu sauran mu ga bākin ƙōƙarin kōwannanku bisa hanyar dangana. Dōmin haka, albarkar Ubangiji ta tabbata a garēku, kuma ga duk wanɗanda suke sama da ƙasa. Dukan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin dūniyōyi.